Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga matasan Nijeriya da su taka rawar gani a yayin zaben shekarar 2027, yana mai cewa sakamakon zaɓen zai yi tasiri matuƙa kan makomarsu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin gangamin zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki da aka gudanar a Jihar Ribas a ranar Asabar.
Da yake jawabi ga matasan a wurin taron, shugaban ƙasar ya ce suna da alhakin taka rawa wajen tsara makomar ƙasar nan ta hanyar shiga cikin harkokin zaɓe.
Ya ce, “Ga matasan Nijeriya, ina kallonku. Wannan zaɓe naku ne, ba nawa ba. Makomarku ta dogara ne da wannan zaɓe.”
Ya kuma buƙaci waɗanda suka yi rajistar zaɓe amma ba su karɓi katin zaɓensu na dindindin (PVC) ba da su je cibiyoyin da aka tanada domin karɓar katunan su.
Tinubu ya bayyana katin zaɓen a matsayin muhimmin kayan aiki wajen tantance shugabannin da za su jagoranci ƙasar.














