ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Samu Sabon Sakamako A Aikin Karkata Ruwa Dake Karkashin Ginawa A Lesotho

by Sulaiman
5 months ago

Babban aikin jigilar ruwa na “Lesotho Highlands Water Project”, ko kuma LHWP a takaice, ya samu sabon sakamako a matakinsa na biyu dake karkashin ginawa, inda a ranar Laraba da ta gabata, aka kaddamar da sabuwar gada ta Senqu, wadda ta kasance wani bangare na aikin.

Wasu kamfanonin kasar Sin ne ke daukar nauyin gudanar da aikin gina LHWP, inda suka samar da guraben aikin yi fiye da dubu 17 ga mutanen wurin, da ba su horo a fannin fasahohin aiki, ta yadda aka mai da aikin LHWP din wani misali na hadin gwiwar Sin da Afirka mai amfanin juna.

Manyan kusoshin da suka halarci bikin kaddamar da gadar Senqu sun hada da sarkin Lesotho, Letsie na uku, da shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa.

ADVERTISEMENT

Cikin jawabin da ya bayar wajen bikin kaddamarwar, sarki Letsie na uku na kasar Lesotho ya ce, sabuwar gadar ta wuce matsayin wata nasara a fannin raya kayayyakin more rayuwa, wadda za ta ba da damar hadewar mabambantan al’ummu, da karfafa hadin gwiwa, da haifar da ci gaban tattalin arziki a dukkan kasashen Lesotho da Afirka ta Kudu.

Kana a nasa bangare, shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta Kudu ya ce, aikin karkata ruwa na LHWP aiki ne da kasarsa ta zuba mafi yawan kudi, cikin dukkan ayyukan da ta samar da kudi wadanda suka kasance a kasashen waje.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Kana ruwan da za a samar ta wannan aiki zai biya bukatar kasar Afirka ta Kudu a fannin raya kasa, ta la’akari da yanayin karancin ruwa da kasar ke fama da shi yanzu. (Bello Wang)

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

Next Post
An Fitar Da Kano Pillars Daga Gasar Federation Cup

An Fitar Da Kano Pillars Daga Gasar Federation Cup

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.