ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tasirin Nasarar Da Kasar Sin Ta Cimma A Fannin Kakkabe Matsanancin Talauci

by Sulaiman and CGTN Hausa
3 weeks ago
Sin

Bayan tsawon shekaru na aiki tukuru, kasar Sin ta cimma nasarar kawar da matsanancin talauci tsakanin al’ummunta. Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar ta kammala dukkanin ayyuka masu nasaba da wannan aiki, ciki har da karfafa nasarori, da fadada matakan yaki da talauci yadda ya kamata, yayin da take kara ingiza farfado da yankunan karkara, da aiwatar da matakan dakile sake tsundumar al’ummun da suka riga suka tsira daga kangin fatara.

Nasarar da kasar Sin ta cimma a wannan yaki, ta baiwa kasar damar cimma kudurin rage fatara, dake cikin ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD, ta nan zuwa shekarar 2030, inda Sin ta cimma wannan kuduri shekaru 10 gabanin wa’adin.

Yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na Sin karo na 14, wanda aka aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, daukacin gundumomin kasar Sin 832 da suka fice daga kangin talauci sun riga sun samar da masana’antu masu tasiri biyu zuwa uku, tare da samar da kudaden shiga da jimillarsu ta haura kudin Sin tiriliyan 1.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 250.77. Hakan a cewar masana, na nuni ga yadda gwamnatin Sin ta cimma nasarar sauya matsayin yankunan karkarar kasar wadanda a baya suka sha fama da fatara, lamarin da ya zamo misali mai gamsarwa na yadda wata kasa ta cimma nasarar warware matsalar raya kai yadda ya kamata.

ADVERTISEMENT

A daya bangaren kuma, baya ga nasarorin da kasar ta Sin ta cimma a cikin gida, tana kuma yin hadin gwiwa da sauran kasashe abokan tafiya musamman kasashe masu tasowa, ciki har da na nahiyar Afirka, wajen aiwatar da wasu ayyuka na yaki da talauci, a matsayin gudunmawar kwarewa da ta cimma a fannin.

Ko shakka babu nasarar da kasar Sin ta cimma a wannan fanni, ta nuna cewa sauran kasashen duniya ma musamman masu tasowa, za su iya kawar da matsanancin talauci, idan sun yi koyi da dabarun da Sin din ta aiwatar gwargwadon halin da suke ciki. Duniya ta ga yadda kasar Sin ta gwada basira, da juriya, da hangen nesa, da aiki ba tsayawa wajen cimma nasarar yaki da fatara wanda sakamakonsa ya baiwa kowa mamaki.

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Hakan ne ma ya sanya masharhanta da dama ke ganin lokaci ya yi da sassan kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, za su himmatu wajen koyi daga dabarun Sin na yaki da talauci, domin fitar da jaki daga duma.

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara
  • Sulaiman
    Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta
  • Sulaiman
    Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita
  • Sulaiman
    Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

MASU ALAKA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji
Daga Birnin Sin

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina
Daga Birnin Sin

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Next Post
Sin Ta Ware Kudi Har Yuan Biliyan 99.9 Domin Tallafawa Kula Da Lafiyar Yara A 2026

Sin Ta Ware Kudi Har Yuan Biliyan 99.9 Domin Tallafawa Kula Da Lafiyar Yara A 2026

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.