ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Sani Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Ɗaya Kan Tallafin Ɗalibai A Kaduna – Kwamishina

by Sulaiman and Shehu Yahaya
3 months ago

A kokarin ta na inganta harkar ilimi a fadin jihar Kaduna, Gwamnatin Jihar ta zuba sama da Naira biliyan daya wajen tallafin karatu, lamunin dalibai da sauran shirye-shiryen inganta ilimi cikin shekaru uku da suka gabata, a wani yunkuri na fadada damar samun ilimi ga matasan jihar.

Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da manema labarai a Kaduna, inda ya jaddada cewa ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Uba Sani ta mayar da hankali a kai domin gina ingantacciyar makoma ga matasan jihar.A cewarsa, daya daga cikin manyan nasarorin gwamnatin shi ne rage kudin makaranta da kashi 50 cikin 100 a dukkan manyan makarantun gwamnatin jihar, matakin da ya saukaka wa dubban dalibai da iyayensu nauyin biyan kudaden karatu.

Maiyaki ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe Naira miliyan 493.27 wajen daukar nauyin karatun dalibai 42 a kasashen waje, musamman a muhimman fannoni kamar likitanci, injiniya, kimiyyar kwamfuta, tsaron yanar gizo da sauran bangarorin da ke da muhimmanci ga ci gaban zamani.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, ya ce an ware Naira miliyan 425.52 domin tallafa wa dalibai marasa karfi da ke karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu a fadin Nijeriya.

Yace gwamnatin ta samar da Naira miliyan 105 domin shirin lamunin karatu, yayin da aka sake fitar da Naira miliyan 27.25 don taimaka wa daliban da suka kammala karatun lauya wajen biyan kudin rajistar shiga Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Kasa.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Da yake karin haske kan nasarorin da aka samu, Babban Sakataren Hukumar Tallafin Karatu da Lamuni ta Jihar Kaduna, Farfesa Yahaya Saleh Ibrahim, ya ce sama da dalibai 21,106 ne suka amfana da shirye-shiryen tallafin karatu a fiye da manyan makarantu 40 da suka hada da jami’o’i, polytechnics, kwalejojin ilimi da makarantun lafiya.Ya bayyana cewa Kaduna ta kafa tarihi a matsayin jiha ta farko a Najeriya da ta hada tallafin karatu da tsarin lamunin dalibai a karkashin tsari guda, abin da ya kara bude kofofin ilimi ga dubban matasa.

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 7 A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.