Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya gargadi ’yan siyasar Nijeriya cewa, bambancin yanki ko asali kadai ba zai sake tabbatar da nasarar zabe ba a babban zaben shekarar 2027, yana mai cewa masu kada kuri’a na kara mayar da hankali kan manyan matsalolin kasa maimakon kabila ko yanki.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin ‘Morning Show’ na gidan talabijin na Arise ranar Alhamis, inda ya yi nazari kan sauyin ra’ayoyin siyasa gabanin zaben 2027 da kuma raguwar tasirin biyayya ga yanki wajen yanke hukuncin zabe.
Ya ce tsohuwar fahimtar cewa duk dan takarar shugaban kasa daga Arewacin Nijeriya zai samu kuri’un yankin kai tsaye na kara zama tsohon zance, yana mai cewa yanzu ’yan kasa sun fi yin nazari mai zurfi wajen zabar shugabanninsu.














Discussion about this post