ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Kira Da A Zurfafa Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Yayin Taron Yayata Manufar Baje Kolin CIIE Da Dandalin Hongqiao

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago
CIIE

An kaddamar da babban taron yayata manufofi dangane da bikin baje kolin kasa da kasa na kasar Sin, na hajojin da ake shigowa da su daga sassan ketare ko CIIE, da taron kasa da kasa na dandalin tattauna batutuwan tattalin arziki na Hongqiao ko HQF karo na tara, a jiya Laraba a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

Mahalarta tarukan biyu sun karfafa bukatar amfani da damammaki na musamman, kuma masu karfi da tarukan ke samarwa wajen bude karin kafofin shiga katafariyar kasuwar kasar Sin, da gaggauta bunkasa masana’antun kasashen Afirka.

Da yake jawabi yayin taron, daraktan sashen masana’antu, ma’adanai, sana’o’i da yawon bude ido a hukumar gudanarwar AU mista Ron Osman Omar, ya yi karin haske game da daga matsayin dangantakar Sin da Afirka zuwa hadin gwiwa daga dukkanin fannoni, wanda baya ga amincin siyasa, hakan ya kuma shaida bunkasar hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki da neman ci gaba, yana kuma taka rawar gani wajen ingiza muradun kasashe masu tasowa.

ADVERTISEMENT

Omar, ya kara da cewa dangantakar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin ta kai wani matsayi mai cike da karsashi da zurfi. Kazalika, baje kolin CIIE ya gabatarwa ‘yan kasuwar Afirka da muhimmin dandali, mai samar da kafa ta kara fadada yawan hajojin da ake fitarwa zuwa sassan ketare, da hade su cikin tsarin daga darajar hajoji da ake hada-hadarsu.

A nasa jawabin kuwa, shugaban tawagar kasar Sin a kungiyar AU Jiang Feng, cewa ya yi baje kolin CIIE na Sin shi ne irinsa na farko a duniya da aka tsara musamman domin ingiza shigo da hajoji, wanda kuma ke zama muhimmin dandali na ingiza babban matsayin bude kofar kasar Sin, da raba damammakin neman ci gaba tare da sauran sassan duniya.

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

Jiang Feng, ya kara da cewa a shekarun baya-bayan nan, sannu a hankali kasar Sin na ci gaba da fadada kawar da dukkanin harajin fito kan hajojin kasashen Afirka da ake shigarwa cikin kasar, da saukaka hidimomin kwastam, da kyautata yanayin gudanar da cinikayya, ta yadda hakan zai bayar da damar kawar da shingaye, da fadada kafofin shigar da karin hajojin kasashen Afirka cikin babbar kasuwar kasar Sin. (Saminu Alhassan)

CIIE
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York
  • Sulaiman
    Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu
  • Sulaiman
    Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya
  • Sulaiman
    ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto
CIIE
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

    Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

MASU ALAKA

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York
Daga Birnin Sin

September 21, 2026
Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu
Daga Birnin Sin

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

September 21, 2026
Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

September 21, 2026
Next Post
Ni Yanzu Ɗan Siyasa Ne Mai Zaman Kansa, Ina Damar Alaƙa Da Kowace Jam’iyya – Gwamnan Bauchi

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Darma A Matsayin Minista

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

September 21, 2026
Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

September 21, 2026
Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

September 21, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

September 21, 2026
Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

September 21, 2026
Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

September 21, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

September 21, 2026
Xi Zai Je Ziyarar Aiki A Amurka Daga Ranar 23 Zuwa 25 Ga Watan Satumba

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

Sin Ta Yi Nasarar Noma Nau’o’in Tsirrai 14 A Cibiyarta Ta Binciken Sararin Samaniya

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci