Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Arewacin Nijeriya ne zai fi amfana da sauye-sauyen tattalin arziƙin gwamnatinsa ke yi, musamman cire tallafin man fetur.
Tinubu ya ce sauye-sauyen sun taimaka wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa ayyukan more rayuwa, ilimi da sauran fannoni masu amfani.
Da yake magana ta hannun Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Nentawe Yilwatda, a wani taron manufofin jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, shugaban ya ce ayyuka kamar bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano, NELFUND da manyan ayyukan tituna za su samar da ƙarin damar tattalin arziƙi a Arewa.
Tinubu ya ce, “Arewa ce za ta fi amfana da wannan tattalin arziƙi,” yana mai cewa yankin zai samu damar cinikayya da maƙwabtan ƙasashe.
Shugaban ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa duk da wahalar da matakin ya haifar, ya zama dole domin ceto ƙasar daga ƙarin matsaloli.
Sai dai ƙungiyoyin Arewa Consultative Forum (ACF) da Middle Belt Forum (MBF) sun yi watsi da iƙirarin shugaban.
ACF ta bayyana kalaman a matsayin abin mamaki, tana mai cewa ƙaruwar talauci, rashin tsaro, ƙarancin ababen more rayuwa da matsalolin noma na nuna cewa har yanzu ’yan Arewa da dama na fama da matsaloli.
MBF ma ta ce cire tallafin man fetur ya shafi ’yan Nijeriya a faɗin ƙasar, don haka bai kamata a bayyana shi a matsayin manufar da ta fi amfanar da wani yanki ba.
A gefe guda, jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ce za ta dawo da tallafin man fetur idan ta lashe zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce hakan zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa.
Sai dai wasu shugabannin Kiristocin Arewa suna da saɓanin ra’ayi da masu sukar gwamnatin Tinubu, inda suka ce Arewa ta amfana da ayyukan gwamnati a fannonin tituna, ilimi da lafiya.
Rev. John Hayab ya ce Tinubu ya fi tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Muhammadu Buhari yin aiki, yana mai kira ga ’yan Arewa da su amince da ayyukan da aka gudanar tare da ci gaba da neman gwamnati ta yi ƙarin wasu.
Sai dai ya amince cewa rashin tsaro, talauci da yunwa manyan matsaloli ne da har yanzu ke addabar yankin Arewa.














