Cutar mashaƙo ta ɓulla a wasu yankunan jihohin Filato, Katsina da Kano, inda wasu mutane suka rasu sakamakon kamuwa da cutar yayin da hukumomin lafiya ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta.
A Jihar Filato, mutane 23 sun rasu, yayin da ake zargin mutane 143 sun kamu da cutar a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
A halin yanzu, mutane tara na karɓar magani.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Nicholas Baamlong, ya ce ƙarancin maganin cutar da kuma jinkirin kai marasa lafiya asibiti na daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta.
Ya buƙaci mutanen da ke fama da alamomin ciwon maƙogwaro, zazzaɓi ko wahalar numfashi su garzaya asibiti da wuri.
A Katsina, cutar ta yaɗu zuwa ƙananan hukumomi 30 daga cikin 34 na jihar.
Gwamnatin jihar ta ce an tabbatar da mutane 31 sun kamu da cutar, amma jami’an Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina sun ce kusan mutane 150 da aka tabbatar sun kamu da cutar kuma an kwantar da su, inda 29 suka rasu cikin makonni uku.
A Kano, Gwamnatin Tarayya ta samar da alluran rigakafin cutar mashaƙo guda 650,000.
Sai dai jihar ta ce tana buƙatar kusan allurai miliyan tara domin raba wa dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa (NCDC), ta ce an samu sama da mutane 10,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Nijeriya a bana.
NCDC ta ce ƙarancin yawan mutanen da ke samun rigakafi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa yaɗuwar cutar, musamman tsakanin yaran da ba a yi wa rigakafi ba ko waɗanda ba su kammala alluran da ake buƙata ba.
Jami’an lafiya sun shawarci iyaye da su tabbatar an yi wa ’ya’yansu dukkanin alluran rigakafin da ake buƙata, inda suka bayyana cewa ana iya kare mutum daga kamuwa da cutar ta hanyar rigakafi, kuma gano cutar da wuri na taimakawa wajen samun ingantaccen magani.














