Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Imo da hukumomin tsaro da su gaggauta ceto matafiya, ciki har da wadanda ke shirin fara hidimar kasa ta NYSC, da aka yi garkuwa da su a Jihar Imo.
Atiku, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, ya bayyana sace matafiya 20 a matsayin abin takaici, yana mai cewa yayin da aka samu nasarar ceto wasu daga cikinsu, har yanzu ana tsare da wasu.
Ya ce: “Sace matafiya 20, ciki har da wadanda ke shirin fara aikin hidimar kasa, a Jihar Imo abin takaici ne. An ceto wasu, amma har yanzu wasu na hannun masu garkuwa da mutane. Ina kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Imo da dukkan hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin dawo da duk wadanda ake tsare da su cikin aminci.”
Atiku ya kuma jawo hankali kan ci gaba da tsare sama da dalibai 70 da aka yi garkuwa da su daga al’ummomin Mussa da Lassa a Jihar Borno.
Ya ce: “A Borno, sama da dalibai 70 da aka yi garkuwa da su daga Mussa da Lassa har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane watanni bayan sace su. Bai kamata a manta da wadannan yara ba. Iyalansu sun cancanci samun cikakken bayani kan halin da suke ciki, yayin da jama’a ke bukatar amsoshi.”














