ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kashe Fasto Da Wasu Mutane 3 A Wani Sabon Hari A Binuwai

by Abubakar Sulaiman
59 seconds ago
Fasto

Akalla mutane huɗu, ciki har da wani fasto, sun mutu bayan wasu mahara da ake zargin makiyaya ne ɗauke da makamai sun kai hari a al’ummar Abeda Shitile da ke Unguwar Gaambe-Tiev, Ƙaramar Hukumar Logo ta Jihar Binuwai. Haka kuma, wasu mutane takwas sun jikkata a harin.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Talata, lokacin da ƴan kasuwa da sauran mazauna yankin ke shirin rufe kasuwa. Wani mazaunin yankin mai suna Andy ya shaida wa jaridar Punch cewa maharan sun shafe sama da sa’o’i biyu suna harbe-harbe, suna ratsa wurare daban-daban na al’ummar tare da tilasta wa jama’a tserewa domin tsira da rayukansu.

An bayyana sunayen waɗanda suka mutu da cewa Msoo Chan, da Fasto Terungwa Tyonungo, da Suurshater Iornumbe da Dodo Shingir. An kwashe gawarwakinsu zuwa ɗakin ajiyar gawa da ke yankin, yayin da waɗanda suka jikkata ke samun kulawar lafiya.

ADVERTISEMENT

Mutane takwas da aka ce sun jikkata su ne Kumater Awua, da Miracle Gangera, da Tsetim Terungwa, da Iortyom Helen, da Seember Aondongu, da Kofi Aondosoo, da Chuku Okoro da Orker Iortyom. Sai dai Kakakin Rundunar Ƴansandan Jihar Binuwai, DSP Peter Aondongu, ya bayar da adadin daban, inda ya ce mutane uku ne suka mutu, yayin da wasu biyu ke jinya bayan da farko aka kai mutum biyar asibiti.

Wannan hari ya ƙara jawo damuwa kan matsalar tsaro a Ƙaramar Hukumar Logo, wadda ta sha fuskantar hare-hare a baya. Har zuwa lokacin wallafa rahoton, Ƴansanda ba su bayyana cikakken bayani kan waɗanda suka kai harin ko kuma dalilinsa ba.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Tinubu Ke Yawan Ciyowa Nijeriya Bashi Abin Tambaya Ne – Atiku

Zaɓen 2027: Gwamnan Kano Ya Nemi A Sauya Masa Kwamishinan ’Yansanda Da DPO 18

Fasto
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kammala Kashi 90% Na Titin Jirgin Ƙasan Kaduna – Kano
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi
  • Abubakar Sulaiman
    Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani
  • Abubakar Sulaiman
    Ba Za Mu Yarda Da Maguɗin Zaɓe Ba – Dino Melaye Ya Gargaɗi INEC

MASU ALAKA

Fasto
Manyan Labarai

Yadda Tinubu Ke Yawan Ciyowa Nijeriya Bashi Abin Tambaya Ne – Atiku

November 5, 2026
Zaɓen 2027: Gwamnan Kano Ya Nemi A Sauya Masa Kwamishinan ’Yansanda Da DPO 18
Manyan Labarai

Zaɓen 2027: Gwamnan Kano Ya Nemi A Sauya Masa Kwamishinan ’Yansanda Da DPO 18

November 5, 2026
2027: Zan Magance Matsalar Tsaro, Na Farfaɗo Da Fatan ’Yan Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

2027: Zan Magance Matsalar Tsaro, Na Farfaɗo Da Fatan ’Yan Nijeriya — Atiku

November 4, 2026

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Fasto Da Wasu Mutane 3 A Wani Sabon Hari A Binuwai

An Kashe Fasto Da Wasu Mutane 3 A Wani Sabon Hari A Binuwai

November 5, 2026
An Kammala Kashi 90% Na Titin Jirgin Ƙasan Kaduna – Kano

An Kammala Kashi 90% Na Titin Jirgin Ƙasan Kaduna – Kano

November 5, 2026
Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu

Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Masu Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu

November 5, 2026
Kar Ku Tayar Da Hankulanku, Mun Samo Fetur Fiye Da Lita Biliyan 1.5 – NNPCL

NNPC Ya Samu Koma Baya Bayan Tura N11.14tn Asusun Tarayya Cikin Watanni Tara

November 5, 2026
Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya Na Mata U-17

Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya Na Mata U-17

November 5, 2026
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

Abubuwa 6 Da Za Su Iya Haramta Maka Yin Zaɓe A Nijeriya

November 5, 2026
Fasto

Yadda Tinubu Ke Yawan Ciyowa Nijeriya Bashi Abin Tambaya Ne – Atiku

November 5, 2026
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nemi Hukunta Asibitocin Da Suka Ƙi Karɓar Majinyatan Gaggawa

November 5, 2026
Zaɓen 2027: Gwamnan Kano Ya Nemi A Sauya Masa Kwamishinan ’Yansanda Da DPO 18

Zaɓen 2027: Gwamnan Kano Ya Nemi A Sauya Masa Kwamishinan ’Yansanda Da DPO 18

November 5, 2026
Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

Taron Tattaunawar Magajin Gari Na Duniya Na 2026 A Ningbo Ya Kasance Na Bude Kofa Da Haduwa Da Juna Da Hadin Gwiwar Birane

November 4, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.