Kasar Sin Ta Gabatar Da Matsaya Game Da Matakan Karshe Na Bincike Mai Lamba 301 Kan Tilasta Yin Kwadago Da Amurka Ta Fitar
Game da matakan karshe na bincike mai lamba 301, kan tilasta yin kwadago da Amurka ta fitar, kakakin ma’aikatar harkokin...
Game da matakan karshe na bincike mai lamba 301, kan tilasta yin kwadago da Amurka ta fitar, kakakin ma’aikatar harkokin...
A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce cikin watannin farko na...
Tawaga ta 27 ta jami’an lafiya ta Sin a Saliyo, ta kaddamar da shirin horar da ma’aikatan jinya ko nas-nas...
Tun a farkon bana, ake ta samun karuwar abubuwa cikin kayayyakin da kamfanonin Sin suka samar da ake turawa Turai....
Yau Litinin, saura kwanaki 100 a bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su...
Hukumar kiddidiga ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, ribar manyan kamfanonin sarrafa kayayyaki na kasar ta karu da kaso 18.7 cikin dari a mizanin shekara shekara, a rabin farko na bana. A cewar hukumar, baki daya bangaren ya ci gaba da samun riba mai gwabi a rabin farkon. Kamfanonin, wadanda kowannensu ke samun kudin shigar da ya kai a kalla yuan miliyan 20 a shekara, kwatankwacin dala miliyan 2.95, sun samu jimilar ribar da ta kai yuan triliyan 3.95 daga watan Junairu zuwa Yunin bana. Sai dai, suna ci gaba da fuskantar kalubalen da suka hada da rashin isassun bukatu na kasuwa, rashin wadataccen jarin gudanar da ayyukan, da yanayi mai sarkakiya a wajen kasar, da kuma rashin tabbas kan farashin kayayyaki a kasuwar duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Litinin cewa, a shirye Sin take ta kara karfafa dangantaka da hadin gwiwa da bangarori da dama da Brazil. Shugaban ya bayyana haka ne yayin zantawa da takwaransa na Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ta wayar tarho, inda ya bukaci bangarorin biyu su kara taka rawar gani wajen inganta tsarin shugabancin duniya da daukaka adalci da daidaito a duniya. Xi Jinping ya kara da cewa, ya kamata Sin da Brazil su hada hannu wajen inganta ci gaban hadin kan kasashen BRICS. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Kakakin rundunar sojojin ruwan Sin reshen kudancin kasar laftana Janar Zhai Shichen, ya bayyana a yau Lahadi cewa dakarun rundunar...
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mikawa shugaban kasar Maldives Mohamed Muizzu, sakon murnar cika shekaru...
A yau Lahadi, hukumar lura da ayyukan kandagarkin bala’o’i, da rage tasirinsu da samar da tallafi ta kasar Sin, ta sanar da shirin ko-ta-kwana a mataki na hudu, da nufin tunkarar tasirin ibtila’in da mahaukaciyar guguwa, da ruwan sama kamar da bakin kwarya suka yi a lardin Guangdong na kudancin kasar, a karo na 12 cikin shekarar nan. Bayan aukuwar mahaukaciyar guguwar da aka yiwa lakabi da Typhoon Noul, yanzu haka an aike da tawagogin jami’ai zuwa yankunan da ibtila’in ya shafa, don nazartar halin da ake ciki, tare da taimakawa mahukuntan wuraren da ayyukan sauyawa jama’a matsugunai, da tabbatar da samar musu abubuwan bukata. Rahotanni sun tabbatar da cewa, a yau Lahadi hukumar tsara ayyukan ci gaba da aiwatar da sauye-sauye ta kasar Sin, ta bukaci a samar da kudi har yuan miliyan 100 daga kasafin kudin kasa don tallafawa lardin na Guangdong, ta yadda za a iya gudanar da ayyukan farfado da kayan more rayuwa bayan ibtila’in. Ana kuma sa ran amfani da kudaden wajen gyara hanyoyin mota, da wuraren adana ruwa, da kayayyakin hidimtawa jama’a irinsu makarantu da asibitoci. Ta hanyar aiwatar da wadannan matakai, ana fatan gaggauta sake farfado da harkokin masana’antu, da zamantakewar al’umma kamar yadda aka saba. Mahaukaciyar guguwar mai lakabin Typhoon Noul, ta aukawa lardin Guangdong da safiyar Lahadin nan, inda karfin iskar a kusa da tsakiya ya kai maki 14. Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka karfinta ya ragu daga matakin koli. (Saminu Alhassan)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.