Kakakin rundunar sojojin ruwan Sin reshen kudancin kasar laftana Janar Zhai Shichen, ya bayyana a yau Lahadi cewa dakarun rundunar na PLA da sojojin saman kasar sun gudanar da jerin sintirin hadin gwiwa a sassan tekun kudancin Sin.
To sai dai kuma kasar Philippines, a kokarinta na janyo kasashen ketaren yankin, ta hada abun da ta kira “sintirin hadin gwiwa” a tekun kudancin Sin, wanda hakan ya gurgunta yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin.
Kakakin ya ce dakarun rundunar za su yi duk mai yiwuwa, wajen kare ikon mulkin yankunan Sin, da hakkoki da moriyarta ta teku, kana za su wanzar da zaman lafiya da daidaito a dukkanin yankin. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/