Kamfanonin Waje 4,800 Sun Kara Yawan Jarinsu A Sin Yayin Da Sashen Manyan Fasahohi Ya Samu Gagarumin Ci Gaba
Kasar Sin ta ci gaba da kasancewa wuri mai jan hankulan masu zuba jari daga kasashen waje, inda kamfanoni kusan 4,800 masu jarin waje suka kara yawan jarin da suke zubawa a kasar a rabin farko na shekarar 2026, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar a yau Alhamis. A cikin watanni shida na farko na shekarar, kasar Sin ta samu karuwar kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje da kashi 5.3% a mizanin shekara-shekara, inda jarin waje da ake zubawa kai-tsaye (FDI) wanda ake amfani da shi a zahiri ya kai yuan biliyan 402.1, watau kwatankwacin dala biliyan 59.2. Tsarin zuba jarin waje ya ci gaba da samun bunkasa, inda jarin da aka zuba a masana’antun manyan fasahohin zamani ya karu da kashi 33.2% a mizanin shekara-shekara, wanda ya kai kashi 42.4% na daukacin jimillar da aka zuba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















