Kakakin Majalisar Dokokin Kungiyar Kasashen Larabawa Ya Jinjinawa Kaidojin Da Shugaba Xi Ya Gabatar
Kakakin majalisar dokokin kungiyar kasashen Larabawa Mohammed Ahmed Al-Yamahi, ya yaba da muhimman kaidoji hudu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, dangane da shigar sassa masu ruwa da tsaki cikin ayyukan warware manyan batutuwan dake addabar kasashen Afirka. Al-Yamahi, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, ya ce kaidojin na shugaba Xi, sun kafa muhimmin tsari don inganta warware tashe-tashen hankula ta hanyar siyasa cikin lumana, da mara baya ga zaman lafiya da daidaito, da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da taimakawa wajen ingiza samar da tsaro, da daidaito a matakin shiyyoyi da na kasa da kasa. Jamiin, ya kara da cewa kaidojin hudu, sun samar da ginshiki mai karfi na inganta hadin gwiwa, da goyon bayan juna tsakanin kasashe masu tasowa, da ingiza kokarin shawo kan kalubalen bai daya, da yayata adalci da karin daidaiton odar kasa da kasa. A ranar 13 ga watan Oktoban nan ne shugaba Xi ya gabatar da kaidojin hudu, yayin da yake ganawa a birnin Beijing da shugaban majalisar ministocin kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbe, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin. Kaidojin dai sun dace da bukatar amfani da jagorancin nahiyar Afirka, wajen warware batutuwa da dama, ciki har da wanzar da adalci da doka, da goyon bayan dakatar da tashe-tashen hankula domin samar da zaman lafiya, da magance sakamako da tushen matsalolin nahiyar. (Saminu Alhassan)



















