Firaministan Sin Ya Isa Kasar Tajikistan Domin Fara Da Ziyarar Aiki Da Halartar Taron Kungiyar SCO
A yau Lahadi ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin Dushanbe domin fara ziyarar aiki a kasar Tajikistan, tare da halartar taro karo na 25 na majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice. Li Qiang, ya isa birnin Dushanbe ne bayan kammala ziyarar aiki a kasar Uzbekistan, inda ya zanta da firaministan kasar Abdulla Aripov a jiya Asabar. Yayin zantawar tasu, Li Qiang ya ce Sin a shirye take ta karfafa tsare-tsaren aiwatar da dabarun neman ci gaba tare da Uzbekistan, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin makamashi, da albarkatu, da fasahar AI, da noman zamani da sauran sassa. (Saminu Alhassan)



















