Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa
Muhawararmu ta wannan makon, ta karkata ne kan jin ra’ayoyinku, dangane da jin tsakanin kazantar daki da ta jiki, wacce ta fi cutarwa? SANI ANWAR da MUHAMMAD BAkIR, su ne suka tattaro muku kamar kowane sati. Halima Idris (Ameerah) daga Kaduna kazantar muhalli (Enbironmental Pollution), matsala ce da ke shafar kowa da kowa, ba tare da la’akari da shekaru ko matsayin mutum ba. Illolinta na iya shafar mutane, dabbobi, tsirrai, kai har ma da jariran da ba a haifa ba. Ba kasafai mutum zai iya guduwa daga wannan barazana ba, domin gurbatacciyar iskar da muke shaka na iya shafar lafiyar kowa. Illolin kazantar muhalli kuma, ba su tsaya kan lokaci guda ba, domin wasu daga cikinsu, kan yi wa lafiyar bil’adama da muhalli illa na dogon lokaci. Wannan ya sa ake bukatar kowa ya taka tasa rawar ganin wajen kare muhalli, domin tsaftataccen muhalli na nufin ingantacciyar rayuwa ga al’umma ta yau da kuma al’ummomin da za su zo nan gaba. Abdullahi Bako Gaskiya a nawa ganin, kazantar jiki ta fi illa fiye da ta muhalli, domin ita cutar jiki, wanda abin ya shafa shi kadai za ta cutar duk da hakan ma na iya cutar da iyalinsa, idan yana dasu. Amma cutar muhalli za ta shafi al'umma da dama, wanda hakan na iya kawo annobar da za ta cutar da rayukan mutane da yawa, wanda cutar jiki ko da za ta cutar da mai yin ta, ko ta kai ga rasa rai, shi kadai za ta shafa. Amma ta muhalli, Allah ne kadai ya san yawan wadanda za su mutu. Farhanat Yakubu kazantar muhalli, ta fi cutarwa nesa ba kusa ba, domin ba mutum daya take shafa ba. Idan mutum yana da kazantar jiki, illar na iya kasancewa a kansa ne shi kadai, sannan kuma zai iya magance matsalar ta hanyar tsaftace jikinsa. Amma idan muhalli ya gurbace, kowa na iya fuskantar illar hakan. Iska mai guba na iya haddasa asma, ciwon huhu da cututtukan zuciya, yayin da gurbataccen ruwa ke iya jawo cututtuka kamar kwalara, zazzabin taifot da amai da gudawa. Haka kuma, gurbatacciyar kasa na iya shafar amfanin gona da abincin da muke ci. Saboda haka, kazantar jiki matsala ce da ta fi shafar mutum daya, amma kazantar muhalli matsala ce da ke iya shafar al’umma baki-daya. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Tsabta rabin imani ce”. Wannan yana nuna muhimmancin kula da tsabtar jiki da kuma muhallin da muke rayuwa a cikinsa. Don haka, ya kamata kowa ya taka rawar gani wajen tsaftace muhalli, domin idan muhalli ya kasance cikin tsafta, za mu samu ingantacciyar rayuwa da kariya daga cututtuka. Khadija Aminu (Oum Fadeel) Ni dai a nawa ganin, kazantar jiki ta fi kazantar muhalli cutarwa, dalili kuwa shi ne, kazantar jiki za ta cutar da mutane da dama. A duk yayin da ka shiga cikin mutane, za su rika kyamar ka saboda wannan kazantar, amma shi daki kafin ka yi bako yana daukar lokaci, shi ko jiki kusan a kullum kana zuwa cikin sha’anin mutane. Maryam Ibrahim Batu na gaskiya, kazantar muhalli ta fi cutarwa, dalili kuwa shi ne, ita kazantar muhalli ba mutum daya yake shafa ba. Misali, idan unguwa ta cika da shara ko najasa ko ruwa mai datti ko kuma hayaki, mutane da yawa za su iya kamuwa da cututtuka daban-daban. Amma kuma kazantar jiki, tana farawa ne daga mutum. Idan mutum bai kula da tsaftar jikinsa ba, yana iya cutar da kansa kuma ya taimaka wajen yada cututtuka ga wasu. Habiba Abdullahi, daga Abuja A gaskiya kazantar muhalli ta fi cutarwa. Dalilina a nan shi ne; kazantar muhalli ta fi cutarwa ga dan’adam ko ta hanyar gurbatacciyar iska, ruwa ko abinci, kowanne daga cikin wadannan kan iya jawo wa mutum kamuwa da rashin lafiya. Don haka, a ganina kazantar muhalli ta fi hadari domin ko mutum yana da tsaftar jiki, idan yana rayuwa a cikin gurbataccen muhalli, lafiyarsa na cikin barazana ko shiga hadari. ...



















