ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

by Rabi'at Sidi Bala
55 minutes ago
Kano

A kwanakin baya ne, matashin furodusan fina-finai a masana’antar Kannywood, Sultan Abdulrazak Dorayi ya bayyana kammala gina wani babban gida a cikin unguwarsu ta Dorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale ta Jihar Kano, inda ya kira wajen da suna ‘FIM House’ wato gidan fim.

Kamar yadda Sultan ya yi bayani wannan katafaren gida zai zama wata farfajiyar shirya fina-finai a faɗin Jihar Kano, inda kuma ya ƙara da cewar wannan waje zai rage yawan karɓar haya wajen aiki da masu shirya fina-finan ke yawan yi a faɗin jihar da kewayenta.

A wancan lokacin, an hango manyan masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood ciki har da jarumi kuma shugaban hukumar kula da harkokin fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu Muhammad suna taya abokin sana’ar tasu murnar kammala wannan aiki da suka kira mai matuƙar muhimmanci da suka daɗe suna fatan gwamnati tayi masu, har ma Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa na sada zumunci cewa zai jagoranci buɗe gidan kwanaki 10 daga ranar da ya yi rubutun, haka zalika, sauran jarumai a masana’antar Kannywood sun yi maraba da wannan aiki na Sultan, inda suka goyi bayansa ɗari bisa ɗari.

ADVERTISEMENT

Sai dai tun bayan bayyana kammala ginin da kuma faɗin abin da ake fatan aiwatarwa a cikinsa da Sultan ya yi ne, sai wasu mutane da aka ce mazauna unguwar suka nuna rashin amincewarsu da ci gaba da gudanar da aikin, inda suka ce samar da irin waɗannan wuraren a cikin unguwanni ka iya zama barazana ga tarbiyar yara masu tasowa.

Abin da Sultan ya musanta, inda ya ce ko alama wannan gida na fim ba zai zama wata hanyar lalata tarbiyar yara ba. Sai dai wannan hujjar ta mamallakin gidan ba ta isa ta hana mutane tunkarar hukumar da ke yaƙi da gina-gidaje ba kan ƙa’ida ba ta Jihar Kano (KANGIS) domin ta shiga cikin lamarin.

LABARAI MASU NASABA

Zulum Ya Bayar Da Cak Na Naira Biliyan 5.81 Domin Biyan Bashin Garatutin Ma’aikata Masu Ritaya

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

A ranar Laraba, 24 ga watan Yunin shekarar 2026, hukumar yaƙi da gine-gine ba bisa ƙa’ida ba a ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na hukumar, Dakta Dalhatu Aliyu Sani, ya jagoranci jami’an da suka je wurin tare da bayar da umarnin rufe cibiyar har sai abun da hali ya yi.

A cewarsa, matakin ya biyo bayan koke da wasu mazauna Dorayi suka kai wa hukumar, inda suka zargi cewa an gina ‘Film House’ ne ba tare da bin ƙa’idojin da aka tanada na tsara gine-gine da ci gaban birane a yankin ba.

Bayan hakan ta faru, mamallakin katafaren ginin ya fito fili ya bayyana cewar ya fasa aiwatar da abin da tun da farko ya yi niyar yi a ‘FIM House’, a maimakon haka zai canza ra’ayinsa zuwa wani abun na daban ko kuma ya siyar da ginin idan buƙatar hakan ta taso.

Amma babbar tambayar da har yanzu mutane ke neman samun amsarta ita ce, me ya janyo aka ƙi yin maraba da ‘Fim House’ a Jihar kano?

Jihar Kano ita ce babbar kasuwar harkar fim a arewacin Nijeriya, inda hasashe ya nuna cewa kaso 80 na fina-finan da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ke gudanarwa tana yin su ne a cikin jihar.

Wanda ake ganini cewa Jihar Kano ita ce sanadiyar da masana’antar ta samo sunanta na Kannywood, manyan fina-finan da suka yi tashe a masana’antar a zamanin baya da yanzu duk a Jihar Kano aka gudanar da su.

Haka zalika, manyan jaruman masana’antar mafi yawancinsu ƴan asalin Jihar Kano ne, tun daga kan Rabilu Musa Ibro, Ibrahim Mandawari, Kabiru Mai Kaba, Ado Ahmed Gidan Dabino, Hamisu Iyan Tama, Hauwa Dan Kano, Saratu Gidado dukkansu haifaffun ƴan Kano ne da suka bayar da gudunmawarsu a ɓangaren jarumai wajen saka Jihar Kano alfahari a ɓangarori da dama.

A ɓangaren bayan kyamara kuwa, akwai manyan masu shirya fina-finai ƴan asalin Kano irinsu AS Mai Kwai, Malam Kato, Malam Aminu Saira, Falalu Dorayi da suka taka muhimmiyar rawa wajen samar wa jihar kuɗaɗen shiga da samar da ayyukan yi ta wannan ɓangaren na shirya fina-finan Hausa.

Yayin da wasu ke ganin akwai dalili na siyasa wajen dakatar da wannan babban aiki da aka shafe tsawon lokaci ana ginawa, wasu kuma na ganin hakan daidai ne a wannan zamani da fina-finai ke da tasiri wajen lalata tarbiyar yara ƙanana. A ɗaya gefen kuwa, wasu na ganin babban abin da ya janyo aka dakatar da wannan aiki bai wuce hassada da wasu daga cikin mazauna unguwar da kuma abokan sana’ar Sultan suke yi masa ba.

Waɗanda ke ganin wannan aiki ya dakata sakamakon siyasa sun kafa hujjarsu akan cewar mamallakin wannan gini baya tare da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a siyasance, hakan ya tabbata bayan Sultan ya nuna sha’awar tsayawa takarar siyasa a wata jam’iyyar ta daban da wadda Gwamna Abba yake a cikinta. Su kuma waɗanda ke danganta rashin nasarar aikin da barazana ga tarbiya, sun kafa hujjarsu kan cewa bai kamata a gina makamancin irin wannan waje ba a unguwa irin Dorayi da dubban mutane ke zaune tare da iyalansu. Sun zargi cewa matukar za a dinga kawo ɗaruruwan jaruman fina-finai domin shirya fim a wannan gida akwai yiwuwar yara ƙanana su yi koyi da wani abu marar kyau da za su dinga gani ana aikatawa a cikin fina-finan sakamakon ƙuruciya duk da cewa su masu shirya fina-finan sun yi ne saboda faɗakarwa.

Sai kuma ɓangaren da suke ganin duk wannan abin ya faru ne sanadiyar wasu daga cikin mazauna unguwar Dorayi da ke da haɗin gwuiwa da wasu cikin abokan sana’ar Sultan da suke yi mashi hassadar ci gaban da ya samu, na zama mutum na farko da ya fara gina irin wannan wajen da niyyar aiwatar da harkokin shirya fina-finan Hausa a faɗin arewacin Nijeriya. Sun kuma yi amanna kan cewa muddin babu hassada, to babu wani aibu a tattare da wannan aiki da Sultan ya shirya yi, hasalima wannan gini idan ya tabbata zai samar wa gwamnatin Jihar Kano kuɗaɗen shiga da kuma rage yawan masu zaman kashe wando a jihar da Nijeriya baki ɗaya.

Kano
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A

MASU ALAKA

Zulum Ya Bayar Da Cak Na Naira Biliyan 5.81 Domin Biyan Bashin Garatutin Ma’aikata Masu Ritaya
Labarai

Zulum Ya Bayar Da Cak Na Naira Biliyan 5.81 Domin Biyan Bashin Garatutin Ma’aikata Masu Ritaya

July 5, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Labarai

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 5, 2026
Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata
Labarai

Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata

July 5, 2026

LABARAI MASU NASABA

Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

July 5, 2026
Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

July 5, 2026
Zulum Ya Bayar Da Cak Na Naira Biliyan 5.81 Domin Biyan Bashin Garatutin Ma’aikata Masu Ritaya

Zulum Ya Bayar Da Cak Na Naira Biliyan 5.81 Domin Biyan Bashin Garatutin Ma’aikata Masu Ritaya

July 5, 2026
Jam’iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya – Hajiya Khadija

Jam’iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya – Hajiya Khadija

July 5, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 5, 2026
Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata

Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata

July 5, 2026
Ba Mu Yarda Da Maƙiyanmu Ba, A Shirye Muke —Iran

Ba Mu Yarda Da Maƙiyanmu Ba, A Shirye Muke —Iran

July 5, 2026
Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

July 5, 2026
LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

July 5, 2026
Enekweci Ne Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya A Wasannin Commonwealth Na Bana

Enekweci Ne Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya A Wasannin Commonwealth Na Bana

July 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.