Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba game da ma’auratan da ba sa iya rike sirrin iyalansu. Akwai ma’auratan da idan suka samu sabani da iyalansu ya zame musu dole sai sun sanar da abokansu matsalar komai kankantarta. Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko me ya sa wasu ma’auratan ba sa iya rike sirrin gidansu ko na iyalansu, kuma me yake janyo hakan?, Wadanne irin matsaloli hakan zai iya haifarwa?, Wacce hanya za a bi domin magance matsalar?”
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aisha Sani, Jihar Kaduna:
Gaskiya dai wasu mazan ba sa iya rike sirri ko kadan, dan yanzu mata sun hankalta an sha su, sun warke domin a baya sun sha baza sirrikansu karshe sai dai a ga mace ta je ta aure mijin, ko kuma an ziga ta kan hanya mara kyau sun bata da miji ya sake ta to, mata da yawa sun hankalta mazan ne dai har yanzu wasu ba hankalin hangen abin da zai iya faruwa. Dan wani namiji wallahi shi irin wannan matar yake so domin ko da ya fadi halinta mara kyau zai fadi me kyau ba tare da ya san shi abokin nasa a wajensa wannan halin nata me kyau ne a wajensa ba, ba mamaki tafi matarsa kyan halaye amma ya boye nasa sirrin bai fada masa sai dai ya ji nasa.
Sunana Lawan Ismail (Lisary), Rano, daga Jihar Kano:
Neman saukin damuwar jin zafin abin da ya faru ne yake jaho hakan. Eh! akwai ta, domin za a rika kallon su ma’auratan kodayaushe cikin matsala a tsakaninsu ko da kuwa suna zaune kalau ne. Hanya daya ce, su yi kokarin guje wa cikin shiga matsalar. Sannan su rika tsayawa suna sanar wa da junansu matsalar tun kafin abin yayi nisa. Shawarata a nan ita ce su daina kokarin fada wa wasu matsalar abokan zamansu, idan har sun kasa dakatar da ita a tsakaninsu idan hakan ta kasance su rika sanarwa da magabatansu, domin neman maslaha. Allah yasa mu dace, Amin.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:
Lallai kuskure ne babba, ga ma’aurata su rika yada sirrin iyalinsu, ko su rika aibata abokan zamansu, kamar miji ko mata, a wajen wasu kamar abokai ko kawaye. Yada sirrin iyali haramun ne a musulunci, kuma kuskure ne na zamantakewa, domin kai za ka iya mantawa amma su ba lallai su manta ba. Za su cigaba da kallonta ko shi da wannan mummunan halinta da ka nuna musu. Yana da muhimmanci mu rika mutunta iyalinmu, kuma mu rika tsare hakkokinsu a gida da idanun jama’a. Mata sutura ne a gare mu, mu ma sutura ne a garemu. Yana da kyau a duk lokacin da aka samu sabani, bayan an samu natsuwa sai a zauna a tattauna a sasanta ba tare da an tozarta juna ko an shigar da wani cikin abin da yake sirrinku ne. Shigar da wani cikin sirrin gidansu, babbar baraka ce a tsakanin iyali. Ina fatan za mu rika hakuri da juna, mu zauna lafiya da iyalanmu. Allah Ya taimake mu bakidaya.
Sunana Amina Yakub, Jihar Kano:
Abin da yake janyo hakan rashin sanin me zai je, ya zo ne. Domin walau mace walau namiji in suka fitar da zancensu shikkenan sun tonawa kansu asiri, dan wani babban burinsa ya ji ba sa zaman lafiya, da zarar ya ji zai kasance cikin farinciki tare da nemo wasu hanyoyin da zai ci gaba da tarwatsa musu zaman aurensu, domin makiya ba su da kama. Fayyace sirri ga abokai na sakawa kowa ya rika yi muku kallo mara kyau, ko da kuna cikin farinciki da juna za a ci gaba da kallonsu da wannan sabanin kuma a ci gaba da yadawa a gari. Abin da mutane ba sa ganewa shi ne, muddin ka fadawa mutum daya sirrinka to, tamkar ka fadawa mutum dubu ne.
Sunana Comr, Nr.Ibrahim Lawan Stk
Dalilai da dama wanda suka hada da rashin hawuri, son samun tausayi, raunin imani, da rashin samun wanda za a tattauna da shi a gida. wasu kuma suna tunanin aboki zai ba da shawara mai bullewa. Yana kawo kunya, raba aure, rashin amana, tsoma bakin mutane, da girmama matsalar, haka zalika sirrin gida ka iya zama labarin kowa da kowa a cikin gari. Hanyoyi da za a magance faruwar hakan ya hada da magana tsakanin miji da mata, neman shawarar manya na gari, rokon Allah, da koyon hakuri, sannan ba kowacce matsala bace aboki ya kamata ya sani ba, musamman a tsakanin ma’aurata don kauracewa gori da abin magana a tsakani idan an samu sabani. Ya kamata ma’aurata su sani cewa aure ya kunshi canjin rayuwa, amana a zamantakewa, sirri, hakuri, gaskiya da biyayya da koyarwa tare da tarbiyya ga dokoki, da kuma umarnin addinin musulunci, sannan ka zabi mutum daya, na gari a matsayin mai shawara, ba kowa ba, ka da ka tona asirin matarka ko yara, haka zalika matar aure ita ma kada ta kasance mai tonan asirin mijinta da yaranta dama nata a karan kanta.
Sunana Abubakar Usman, Malam Madori, A Jihar Jigawa:
Wasu maza ba sa iya rike sirrin gidansu ne saboda rashin sanin-kai da kuma rashin zurfin tunani, da kuma son goyon bayan abokai, sau tari rashin ilimin zaman aure, da kuma tasirin tarbiyya, Hakan kan jawo matsaloli kamar kara rura wutar rikici, da rage mutunci, da kuma rashin amincewa tsakanin ma’aurata, har ma ya iya kaiwa ga rabuwa. Don magance wannan matsala, ya kamata a inganta mu’amala da kawaici tsakanin ma’aurata, a koyi rike sirri, a guji yanke hukunci cikin fushi, sannan a nemi shawara daga mutanen da suka dace kawai idan ya zama dole. Shawara ta ga masu aikata hakan su ji tsoron fallasa sirrin gida, su yi hakuri da juriya, su tattauna da matansu cikin hikima, kuma su yi kokarin gyara kansu domin samun zaman lafiya mai dorewar aure.
Sunana Sa’eed Sulaiman, Mallam madori, A Jihar Kano:
A gaskiya rashin sanin kai ne da kuma kimar aure da zamantakewa. Hakan kuma yakan haifar da rashin aminci ga juna da kuma karancin girmamawa ga magidanta hatta wadanda ake bayyanawa sirrin ba za su ga kimar magidancin ba. Mafita shi ne a koma ga koyarwar ma’aiki na tsarin zamantakewa da iyali tare da fadakar da juna da nuna rashin dacewar hakan. Shawarar da ya kamata ita ce shirya bita akan zamantakewar auren da kuma fadakarwa cikin hikima ga masu aikata hakan.
Sunana Anas Bn Malik, Achilafiya Ƴankwashi, A Jihar Jigawa:
Tabbas Akwai, hakan na faruwa saboda neman goyon baya, fushi, rashin rashin sanin muhimmancin sirrin aure. Bayyana matsalolin gida kan rage mutuncin iyali da kuma haifar da rashin amincewa tsakanin ma’aurata. Haka kuma, yana iya janyo tsoma bakin mutane da kara rikita al’amura. Sirrin da ya fita daga gida ba ya komawa, ko bayan an sasanta matsalar. Don magance hakan, ya kamata ma’aurata su rika tattaunawa cikin natsuwa da fahimtar juna. Idan akwai bukatar shawara, a nemi masu hikima da rikon amana maimakon kowane aboki. Maza su tuna cewa kare sirrin iyalansu wani bangare ne na amana da nauyin aure. Kiyaye sirrin gida yana taimakawa wajen samar da zaman lafiya da dorewar soyayya a tsakanin ma’aurata.
Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:
Akwai su, wani ba ya iya rike sirri, wani kuma yana iyawa. Wani yana ganin yana da aboki ba zai iya boye masa komai ba, wani kuma ba haka yake ba. Kai za ka iya fada masa amma shi ba zai taba fada maka sirrinsa ba, ya danganta. Matsala kuwa idan Allah ya sa wani sabanin ya shiga tsakani ya fada masa sirrinsa gori zai yi masa. Shawara ya kmata mutum ya iya rike sirrinsa hakan zai fi rufin asiri. Sai kuma sirrin da ya kasance na halin rayuwa za ka iya fadawa na kusa da kai ko wanda ka yarda da shi, amma ba kowane sirri ake fayyacewa ba.
Sunana Munzali Bala Musa (Baba Nababa Zabi Biyu), Adakawa, Dala LGA, Jihar Kano:
Shawara zuwa ga maza, ka zama mai iya rike sirrinka, domin sirrinka sirrinka ne kai kadai aboki mahallinsa daban don haka shi ma sirrin gidanka shi ma mahallinsa daban.
Sunana Buwangal, Adamawa:
Maza da yawa ba sa rike sirrin aure saboda rashin hakuri da neman shawara daga abokai, hakan yana haifar da kunya, fada, da lalata mutuncin gida, maganin shi ne ma’aurata su magance matsala tsakaninsu, ko su nemi malamai/masu shawara maimakon abokai. shawara ka ji tsoron allah, gida sirri ne, ka gyara da matarka da kanka, kada ka tona asiri.















Discussion about this post