Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Alhamis ya bukaci Rundunar Sojin Nijeriya da ta daina kallon aikinta a matsayin...
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Alhamis ya bukaci Rundunar Sojin Nijeriya da ta daina kallon aikinta a matsayin...
A yau Alhamis, an gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kungiyar hadin gwiwar fasahar kirkirarriyar basira ta AI...
Jam'iyyar (ADC) ta sake shiga cikin rikicin cikin gida bayan daya daga cikin fitattun jagororinta, Salihu Mohammed Lukman, ya sanar...
A kwanan baya, kamfanin Nearpays na kasar Najeriya ya lashe kyaututtuka a Afirka da ma duniya baki daya, saboda manhajar biyan kudi ta wayar salula da ya tsara, wadda ta kunshi fasahar kirkirarriyar basira ko AI. Wani abu na musamman da ke cikin wannan manhajar shi ne yadda ya iya aiki ba tare da amfani da yanar gizo ko Intanet ba, wanda ke ba mutane damar biyan kudi ta wayar salula, ko da a yankunan karkara masu nisa inda ba a samun siginar wayar salula. Wannan hanyar amfani da fasaha wajen inganta rayuwar jama’a ta yi daidai da ka'idar amfani da fasahar AI ta Majalisar Dinkin Duniya ta "Fasaha mai fifita al’umma, amfani da AI ta hanyar da ta dace", kuma ra'ayi ne da kasar Sin ke kokarin aiwatarwa a fannin raya fasahar AI. A kasar Sin, babban burin da ake neman cimmawa ta hanyar amfani da fasahar AI shi ma ya kasance samar da hidimomi ga jama’a. Idan aka dauki misali da bangaren kula da lafiya, a wasu asibitoci na matakin unguwanni a birnin Beijing, na’urorin aiki masu kunshe da fasahar AI na iya taimaka wa marasa lafiya tsara shirin ganin likita, da tantance cututtukan ido, da kuma taimaka wa likitoci wajen neman bayanan tarihin jinya, da tantance hotunan da aka dauka ta na’urorin bincike, da kuma kula da magunguna. Ta wannan hanya, an daidaita aikin jinya a asibitocin, da kuma samar da sauki ga marasa lafiya. A zahiri, "Dora mihimmanci kan moriyar jama’a" wani tunani ne na bai daya na Sin da Afirka ta fuskar fasahar AI. Sai dai mabambantan kasashe su kan samu ra’ayoyi masu bambanci. Misali, yanayin da ake ciki a Amurka ya bambanta. Cikin wata makalar da ya rubuta, masanin ilimin al’amuran duniya dan kasar Kenya Elijah Mwangi ya bayyana bambanci da ke tsakanin salon kasar Sin da na Amurka a fannin raya fasahar AI. Ya bayyana cewa dabarar raya fasahar AI ta Sin ta shafi manufar sanya gwamnati ta rika ba da jagoranci, da kokarin samar da na’urorin zamani a matsayin ababen more rayuwa, yayin da Amurka ke bin tsarin jari-hujja. Wato masana'antun fasahar AI na Amurka galibinsu manyan kamfanoni ne ke kula da su bisa tsarin kasuwanci. A ganin wadannan kamfanoni, damar samun riba da takara da kamfanonin sauran kasashe, sun fi bauta wa jama’a muhimmanci. Idan aka dauki fannin kiwon lafiya a matsayin misali, Amurka tana kokarin amfani da fasahar AI wajen inganta wani tsarin kiwon lafiya mai tsada, maimakon bai wa talakawa damar samun hidimomi masu araha. Wannan babban bambanci ne ya sa kasar Sin fara gabatar da manufar kula da ayyukan raya fasahar AI mai amfanar da al’ummun duniya, wadda ta kunshi ra’ayoyin "Raya fasahar AI don samar da alfanu, da tsaro, da adalci", da "Ba da taimako ga kasashe masu tasowa" , da "Tabbatar da wakilcin kasashe masu tasowa a fannin kula da fasahar AI", da sauransu. Daga gabatar da "Shawarar kula da harkoki masu alaka da fasahar AI na duniya" , zuwa aiwatar da "Shirin raya fasahar AI mai amfanar da kowa", kasar Sin tana kokarin mai da fasahar AI wani lamari da zai amfanar da dukkan bil'adama. A lokacin da ake magana kan fasahar AI ta kasar Sin, masana ilimin kimiyya da fasaha ’ya’yan Afirka su kan yaba mata bisa yadda take da araha. Elijah Mwangi ya ce, karfin kasar Sin a fannin kera kayayyaki, ya sanya ta zama bangare mai muhimmanci dake samar da hidimomi masu araha ga masu amfani da fasahar AI. Wannan ya saukaka wa kasashen da ke son amfani da fasahohin zamani kuma a farashi mai rahusa. A nasa bangare, Lawrence Nderu, wani shehun malami dake aiki a jami'ar kimiyya da fasaha masu alaka da aikin gona ta Jomo Kenyatta ta kasar Kenya, ya yaba wa manhajojin fasahar AI na kasar Sin, wadanda suka zama “Open Source”, wato nuna dukkan bayanan tsara manhaja ba tare da boye su ba. Ya ce bisa amfani da wadannan manhajojin kasar Sin, kungiyoyi masu tsara manhaja na kasashen Afirka za su iya kara dogaro da kai, da kare bayanai masu mahimmanci, da kuma samar da dabarun daidaita matsalolin da ake fuskanta a kasashen Afirka. Yadda ake amincewa da tunani da fasahohi masu nasaba da AI na kasar Sin shi ma ya inganta hadin gwiwar Sin da Afirka. A Afirka ta Kudu, kamfanonin kasar Sin sun ba da taimako wajen daidaita tsarin kula da zirga-zirgar jiragen kasa, wanda ya tabbatar da tsaro. A Djibouti, tsarin ba da gargadi don kandagarkin bala’i na "MAZU-Urban", wanda hukumar kula da ayyuka masa alaka da yanayi ta kasar Sin ta bayar kyauta, ya taimaka wajen rage mummunan tasirin bala’i daga Indallahi ga tattalin arziki da rayuwar mutane. Wadannan lamuran sun nuna cewa "dora muhimmanci kan moriyar jama’a" ra’ayi ne na bai daya na Sin da Afirka dagane da aikin raya fasahar AI. Bugu da kari, wannan ra’ayin ya tabbatar da kyakkyawar makoma ga yunkurin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. (Bello Wang)
Sakamakon wani binciken da kafar yada labarai ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ta...
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei, ya yi kira da a kafa wani tsari na duniya na...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai kasance babban mai gabatar da jawabin buɗe taro a Taron Ƙasa da Ƙasa na...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian, ya ce a halin yanzu an hada tsarin samar da kayayyaki da na...
Shahararren marubucin Amurka, kuma masanin fasahar Intanet, kana mai hasashen makoma Kevin Kelly, a kwanan nan ya yi hira ta musamman da wakilin CMG, inda ya yi tsokaci kan rawar da fasahar AI za ta iya takawa a fagen ilimi a nan gaba. Ya bayyana cewa, AI na iya taimakawa wajen cimma burin ba da ilimi na "koyar da dalibai daidai da kwazonsu", ta yadda tsarin ilimi zai dace da kowane dalibi bisa yanayinsa. Kevin Kelly ya kuma ce, a Sin ko a Amurka, ko a wasu sassan duniya, daya daga cikin burin ba da ilimi shi ne a iya koyar da kowane dalibi bisa la'akari da kwazonsa. Ya ce, “Muna da burin ganin an iya fitar da irin tsarin koyarwa na musamman, amma duba da cewa malami daya ke da nauyin kula da dalibai 30, ba zai iya cimma wannan buri ba sai ta hanyar taimako daga AI. Don haka, fasahar AI na iya zama "mai koyarwa", wadda za ta taimaki dalibai da dabarun koyo da kuma bincika ilimi bisa la'akari da saurin koyonsu da kuma sha'awarsu. (Amina Xu)
Majalisar Dattawan Nijeriya ta buƙaci Babban Hafsan Sojin Ƙasa da Sufeto Janar na ’Yansanda da su gaggauta tura ƙarin jami’an...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.