Pate Ya Jinjina Wa Sauye-sauye Da Inganta Harkokin Lafiya A Katsina
Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko...
Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko...
An bude bikin fina-finai na kasa da kasa na hanyar siliki karo na 13 a birnin Xi’an na lardin Shaanxi...
Kano Pillars, wato Masu Gida, za su kara da Doma United a filin wasa na Sani Abacha Stadium ranar Lahadi,...
An bude gasar wasannin motsa jiki ta Asiya karo na 20 a birnin Nagoya na lardin Aichi na Japan da...
Kasar Sin ta samu tafiye-tafiyen biliyan 3.32 na jiragen kasan jigilar fasinjoji cikin watanni 8 na farkon bana, adadin da ya karu da kaso 3.9 kan mizanin shekara-shekara. A cikin watannin, matsakaicin adadin tafiye tafiyen jiragen kasa masu jigilar fasinjojin ya tsaya kan 11,508 a kullum, wanda ya karu da kaso 5 kan na bara. (Mai fassara: Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
An rantsar da Alhaji Bala Adamu Milton a matsayin Shugaban Riƙo na Ƙungiyar Gamayyar ’Yan Kasuwa ta Jihar Kaduna, wato...
Fu Cong, zaunannen wakilin Sin da ke MDD, ya bayyana cewa ana gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na...
An gudanar da dandalin tattaunawa na jama’a na WTO na 2026 na kwanaki uku a birnin Geneva na Switzerland. A...
A yau Asabar, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya amsa tambayoyin da wasu kafofin yada labarai suka yi, dangane da muhawarar bangarorin Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya. A cewar kakakin, bisa tattaunawar da bangarorin Sin da Amurka suka yi, Mista He Lifeng, mataimakin firaministan kasar Sin, zai jagoranci wata tawaga wajen gudanar da shawarwari tare da bangaren kasar Amurka, kan batutuwa masu nasaba da tattalin arziki da cinikayya, tsakanin yau 19 da 23 ga wata, a kasar Amurka. Kakakin ya kara da cewa, bangarorin Sin da Amurka za su yi muhawara bisa tushen matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a baya. Ban da haka, a kwanan baya, wasu kafofin yada labaru sun ba da labarin cewa, kungiyar kasashen Turai ta EU na fatan cewa kasar Sin za ta takaita fitar da motoci kirar kasar masu amfani da mabambantan makamashi zuwa kasashen Turai, sa'an nan idan kasar Sin ta ki daukar wannan mataki, to, za ta iya fuskantar karin harajin fito. Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya ce, wannan mataki na takaita fitar da kaya ya zama karya ka'idojin kungiyar ciniki ta duniya WTO, wanda kuma bai dace da al'adar kasuwanci, da ka'idar yin takara cikin adalci ba. Saboda haka kasar Sin ba za ta amince da shi ba. Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, bangaren Sin bai taba sauya matsayinsa ba, wanda shi ne, dole a tabbatar da daidaiton moriyar kowa, da bin ka'idojin kungiyar WTO da dokokin kasashe daban daban, da kokarin kare moriyar kamfanonin Sin da na kasashen Turai, yayin da ake tsara dabarar daidaita sabanin ra'ayi tsakanin kasar Sin da kungiyar EU. (Bello Wang)
A kwanan baya, shugaban majalisar dokokin kasar Angola, Mista Adao Almeida, ya yi ziyarar aiki a kasar Sin. Yayin da yake hira da wakilin kafar CMG, Mista Almeida ya ce, kasar Sin tana da shugaba mai hangen nesa, wanda yake kulawa da al'ummar kasar cikin tsanake. A cewar Almeida, shugaba Xi Jinping na kasar Sin yana da wasu halaye na musamman, kamar dora matukar muhimmanci kan ci gaban tattalin arziki, da fahimtar ainihin kalubalolin da kasar Sin da sauran kasashe daban daban suke fuskanta, da kokarin neman bakin zaren warware matsalolin. A lokacin da ya ambaci shawarwari guda 4 da shugaba Xi ya gabatar a kokarin daidaita al'amuran duniya, Mista Almeida ya ce, wadannan shawarwari suna da amfani ga yunkurin kafa tsarin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, ta yadda za a samar da wani dandali na tattaunawa tsakanin kasashe daban daban, don tsara wasu ka'idoji na bai daya da za su biya bukatun daidaita al'amura, da ba da damar kara dora muhimmanci kan hadin kan al'ummun sassan duniya, maimakon kebabbun kasashe marasa alaka a tsakaninsu. Kana Mista Almeida ya bayyana kasar Sin a matsayin wata babbar kasa, wadda ke taka rawar gani a fannin zamanantar da al'umma, da sauya tsarin masana'antu zuwa na dijital. A cewarsa, dalilin da ya sa kasar Sin samun nasara a fannin raya kasa, shi ne tsarinta na siyasa mai inganci, da cikakken tunanin da ake da shi a fannin raya kasa, da yadda ake aiwatar da manufofi yadda ake bukata. Ban da haka, ingantaccen tsarin kasar na sanya ido kan harkoki daban daban, shi ma ya samar da gudunmowa sosai. Har ila yau, Mista Almeida ya ambaci hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Angola ta fuskar tattalin arziki. Ya ce akwai daruruwan kamfanonin kasar Sin da suke aiwatar da harkokinsu a kasar Angola, wadanda suka zuba jari, gami da kafa rassa a kasar. Kana wasu daga cikinsu sun kwashe shekaru da dama suna kokarin raya harkokinsu a kasar Angola. Ban da haka, dimbin kamfanonin kasar Sin na taimaka wa kasar Angola a yunkurinta na raya sassa daban daban na tsarin tattalin arziki. (Bello Wang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.