An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York
Mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin He Lifeng, da sakataren kudi na Amurka Scott Bessent, da wakilin kasuwanci na kasar Jamieson...
Mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin He Lifeng, da sakataren kudi na Amurka Scott Bessent, da wakilin kasuwanci na kasar Jamieson...
Ma’aikatar raya masana’antu da fasahohin sadarwa ta kasar Sin, ta ce gwamnatin kasar ta sha alwashin zakulowa, da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu da ake da kyakkyawan fatan bunkasarsu. Ma’aikatar ta ce maimakon jiran har sai irin wadannan masana’antu sun nuna bukatarsu ta neman taimako, gwamnati za ta himmatu wajen lalubo su da tallafa musu yadda ya kamata. Karkashin hakan, ma’aikatar za ta kyautata tsarin tallafinta ga irin wadannan masana’antu, musamman masu amfani da fasahohin zamani da kwarewa, ta yadda za su kai ga sarrafa hajoji masu kima da fice tsakanin nau’o’insu, kana za a matsa kaimi wajen lalubo sabbin kamfanoni da ake ganin za su ciri tuta a nan gaba, musamman ma wadanda ke mayar da hankali ga ayyuka masu kunshe da fasahohin kirkire-kirkire, da masu bunkasa sabbin hajoji. A jiya Lahadi ne ma’aikatar ta alkawarta hakan, yayin wani taron masu ruwa da tsaki, yayin tattaunawa dangane da hanyoyin kyautata tsarin bincikowa, da samar da karin hidimomi ga irin wadannan masana’antu. Wani jami’in ma’aikatar ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da inganta tsarin shari’a da manufofin gudanarwa, da shirye-shiryen kyakkyashe masana’antu, da tallafawa ’yan kasuwa da hidimomi ta yadda za a kai ga ingiza ci gaba mai nagarta tsakanin kanana da matsakaitan masana’antu. Kazalika, za a ci gaba da karfafa gwiwar kamfanoni ta yadda za su kai ga cimma muradun kwarewa, da ci gaban kirkire-kirkire, da fadada bincike da samar da ci gaban harkokin zuba jari, da kokarin cimma sabbin nasarori a muhimman fasahohi. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a yau Litinin cewa, a ranar 25...
’Yan bindiga sun kai hari garin Dukura, da ke ƙaramar hukumar Kebbe a Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane biyu...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin kashi 95 cikin 100 na albashin ma’aikatan lafiya a faɗin jihar, inda sabon...
Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta samu tsawon shekaru uku daga hukumomin Saudiyya domin Nijeriya ta dace da sabon tsarin...
Jigon jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya nuna damuwa kan kasancewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a wajen...
Wani jami’i ya bayyana a yau Litinin cewa, ana sa ran jimillar darajar hatsin da za a noma a masana’antar hatsi ta kasar Sin za ta zarce yuan tiriliyan 4.5, watau dala biliyan 666.8, a yayin aiwatar da shirin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 a tsakanin shekara ta 2026 zuwa ta 2030. Shugaban hukumar kula da abinci da tsare-tsaren adanawa ta kasa, Liu Huanxin, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, sashen noma hatsi zai inganta cimma bukatun mutane a bangaren samun abinci mafi kyau, da gina jiki, da kuma lafiya. A shekarun baya-bayan nan, masana’antar hatsi ta kasar Sin ta ci gaba da samun bunkasa ba tare da tangarda ba, inda jimillar darajar hatsin da kamfanonin masana’antar suka noma ta karu daga yuan tiriliyan 3 a karshen shirin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13 (a tsakanin 2016 da 2020), zuwa sama da yuan tiriliyan 4 a karshen shirin karo na 14, watau a tsakanin 2021 zuwa 2025. Liu ya kuma ce duk da kwan-gaba-kwan-baya da ake samu a kasuwar hatsi ta duniya a halin yanzu, kasuwar hatsi ta kasar Sin ta ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali gaba daya kuma an samu tabbaci sosai a bangaren kiyaye wadatar abinci na kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Darajar Hatsin Da Za A Noma A Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 4.5 A...
A rana ta farko ta fafata gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Asiya karo na 20 da ke gudana a...
A yau Lahadi, kasar Sin ta aike da taurarin dan’adam guda tara zuwa sararin samaniya ta hanyar amfani da rokar...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.