Jigon jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya nuna damuwa kan kasancewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a wajen Nijeriya a lokaci guda.
Melaye ya yi wannan tambayar ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce, wa ke gudanar da harkokin ƙasar a halin yanzu?
Shugaba Tinubu ya tafi hutun shekara na tsawon makonni uku, inda ya fara tafiyarsa a London kafin ya wuce Paris na Faransa. Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana tafiyar a matsayin wani ɓangare na hutun shekara na shugaban.
Shi kuwa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tafi New York domin wakiltar Nijeriya a taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda za a gudanar daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumba 2026.
Tambayar Melaye ta shafi yadda ake gudanar da shugabanci a halin yanzu yayin da shugaban da mataimakinsa suke wajen ƙasar a lokaci guda.














