Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta samu tsawon shekaru uku daga hukumomin Saudiyya domin Nijeriya ta dace da sabon tsarin gudanar da aikin Hajji da kasar ke shirin aiwatarwa.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce an samu wannan damar ne bayan tattaunawa da hukumomin Saudiyya.
Ya ce Saudiyya ta fara shirin mayar da kusan kashi 98 cikin 100 na alhazan Nijeriya karkashin kamfanonin yawon bude ido masu zaman kansu, amma Nijeriya ta nuna damuwa cewa sauyin cikin gaggawa na iya kara tsadar aikin Hajji ga alhazai.
Sabon tsarin, wanda ke cikin shirin Saudi Vision 2030, na da nufin kara amfani da fasahar zamani, inganta gudanar da aikin Hajji da kuma mayar da wasu ayyukan kula da alhazai karkashin kamfanoni masu lasisi.
Yusuf ya ce yawancin alhazan Nijeriya mutane ne masu karamin karfi, wadanda ke tara kudi na tsawon lokaci domin samun damar gudanar da ibadar Hajji.
A karkashin yarjejeniyar da aka cimma, kashi 30 cikin 100 na alhazan Nijeriya ne za a fara tafiyar da su ta hannun kamfanonin yawon bude ido masu lasisi a Hajjin 2027, sannan a rika kara adadin a hankali cikin shekaru uku.
NAHCON ta ce tsarin mika alhazan zuwa kamfanoni masu zaman kansu a hankali zai taimaka wajen rage tasirin sauyin tsarin da kuma ba Nijeriya damar shirya tsarin yadda ya dace.














