FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA
Hukumar kwallon ta nahiyar Turai (UEFA) ta soki matakin da hukumar kwallon kasa ta Duniya (FIFA) ta dauka na dakatar...
Hukumar kwallon ta nahiyar Turai (UEFA) ta soki matakin da hukumar kwallon kasa ta Duniya (FIFA) ta dauka na dakatar...
shugabannin Sin da Madagascar sun yi musayar sakon taya murnar cika shekaru 20da kulla alakar diflomasiyya tsakaninsu A yau 6 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musayar sakon taya murna da shugaban Montenegro Jakov Milatović, don murnar cika shekaru 20 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. Bangarorin biyu suna fatan yin amfani da wannan zarafi mai kyau don zurfafa hadin gwiwa mai amfani ga juna, da samar da kyakkyawar rayuwa ga al'ummomin kasashen biyu, da kuma bayar da gudunmawa ga inganta zaman lafiya da ci gaban duniya. (Amina Xu)
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Pankshin/Kanke/Kanam a Tarayya, Yusuf Gagdi, ya nuna adawarsa ga shirin gyaran hali na ’yan...
A yayin taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD(UNHRC) karo na 62, asusun bunkasa hakkin dan Adam na kasar Sin ya shirya wani taron gefe. A gun taron, wani masanin Sin ya yi maganar da ta burge kowa, inda ya ce, "Ma'auni na gaske dake tantance yanayin hakkin dan Adam na wata kasa, ba wani tsari ba ne, sai dai ko al’ummar wannan kasa suna rayuwa da mutunci da tabbaci da kuma ci gaba." Bisa nazarin da aka yi, na ce, tun daga shekara ta 2009, Sin ta tsara da aiwatar da shirye-shiryen raya ayyukan hakkin dan Adam na kasa, wanda hakan ba wai kawai ya nuna alkawarin da ta yi wa al'ummarta da duniya ba, har ma ya samar da abin koyi ga kasa da kasa kan jagorantar harkokin hakkin dan Adam. Alkaluma sun nuna cewa, a shekara ta 2025, jimillar GDP na Sin ya kai sama da Yuan tiriliyan 140, kuma matsakaicin kudin shiga na kowane mutum a ko wace shekara ya kai Yuan 43,377, wanda ya karu da kashi 5.0%, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta. Adadin wadanda suka shiga inshorar ritaya mai tushe ya kai mutane biliyan 1.076, adadin da ya kiyaye matsayin kashi 95%. Karin guraben aikin yi da aka samar a wannan shekara ya kai miliyan 12.67. Yawan masu shiga karatun tilas na tsawon shekaru 9 na kasar ya kuma kiyaye kashi 96.1%, kuma adadin daliban da ke karatu a jami’o’i ko kwalejoji ya wuce miliyan 43. Wadannan alkaluma sun shaida nasarorin da kasar ta samu a kokarinta na tabbatar da hakkin al’ummarta, kuma suna nuna yadda take aiwatar da manufar "sanya muradun jama’a a gaban komai" da kuma kare "’yancin rayuwar Sinawa". A yankin Xizang na kasar Sin, a da yawan mutanen da ke fama da jahilci ya kai sama da kashi 95%, amma yanzu an gina cikakken tsarin samar da ilimi na zamani, kuma ana aiwatar da manufar ba da ilimin kyauta na shekaru 15, wanda ya shafi daga matakin gidan renon yara zuwa sakandare. Tsawon rayuwar mutane a yankin ya kuma karu daga shekaru 35.5 a shekarar 1951 zuwa shekaru 72.19 a yanzu. A yankin Xinjiang na Sin, gwamnatin yankin ta kokarin bunkasa masana'antar noma, kamar noman auduga da kuma noman 'ya'yan itatuwa na musamman, don inganta amfani da filayen karkara da kuma kara kudin shigar manoma. A wasu yankuna, an gina makarantun koyon sana'o'i, inda ake ba da horo na musamman kamar aikin lantarki, aikin gida, da kasuwanci ta yanar gizo, don bai wa manoma da makiyaya damar koyon ilmin masana'antu. Wadannan alkaluma da al’amura na bayyana yadda kasar Sin ke kokarin tabbatar da hakkin dan Adam. Tun bayan kafuwar kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD shekaru 20 da suka gabata, har yanzu akwai sauran rina a kaba wajen kula da hakkin dan Adam na duniya. Ayyukan kare hakkin dan Adam na Sin sun ba da mafita madaidaiciya, wato hakkin dan Adam ba hujjar sukar sauran kasashe ba ne, a'a, dabara ce ta samun ci gaba, wato misali girbin gona da kudin shigar jama'a da karatun yara a makarantu, kana da ayyukan yi masu dorewa da ingantuwar rayuwar al’umma. Misalin da Sin take bayarwa dangane da rayuwa da muradun jama’a, ya zama mai ma’ana wajen murnar cika shekaru 20 da kafuwar kwamitin. Wannan kuma ita ce mafi kyawun matakin dake bayyana "Hakkin dan Adam na dukkan bil'adama". (Marubuciya: MINA)
ADC Ta Rushe Shugabannin Jam’iyyar a Kano, Ta Naɗa Kwamitin RiƙoJam’iyyar ADC ta rushe kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a Jihar...
Rundunar sojin ruwa ta kasar Sin, ta ce wani jirgin ruwanta mai nutso mai makaman nukiliya, ya yi nasarar harba...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya miƙa saƙon ta'aziyya...
An kaddamar da atisayen hadin gwiwa mai taken “Hadin gwiwar ayyuka kan teku-2026” tsakanin Sin da Rasha a wata tashar...
A yau Lahadi 5 ga watan nan na Yuli, dakin nune-nunen shaidun dake tabbatar da ta’asar aikata laifukan yaki, da...
A kwanakin baya, an gabatar da littafin “Bayanan Xi Jinping kan basirar gudanar da ayyuka a kananan hukumomi” a dukkan...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.