Rundunar sojin ruwa ta kasar Sin, ta ce wani jirgin ruwanta mai nutso mai makaman nukiliya, ya yi nasarar harba wani makami mai linzami mai dauke da abun fashewa na gwaji, zuwa wani yankin ruwan tekun Pasifik da ba ya karkashin ikon wata kasa, kuma ya sauka a daidai inda aka tsara zai sauka a cikin ruwan.
A cewar rundunar, wannan gwaji ne da aka saba yi a kowace shekara, kuma kasar Sin ta sanar da kasashe masu ruwa da tsaki kafin lokacin gwajin.
Haka kuma, gwajin ya dace da dokar kasa da kasa, kana ba a yi shi don wata kasa ko wani abu ba. (Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/