ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Za A Kai Ga Fahimtar Aikin Kawar Da Talauci Na Kasar Sin Ba In Dai Ba Rikon Gaskiya

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago

Kwanan baya, jaridar Financial Times ta Birtaniya ta buga wata makala mai taken “Sin ta yi ikirarin kawar da talauci, shin da gaske ta yi hakan?” Makalar ta mayar da hankali kan aikin “Yaki da Talauci” da nasarorin da kasar Sin ta samu, wadda tamkar gaskiya ta bayyana, musamman ta yin la’akari da shaidun da ta samar da ma hotunan da ta dauka.Sai dai yadda marubucin ya musanta nasarar a zo a gani da kasar Sin ta cimma ta fannin rage talauci, bisa wasu misalai kalilan da ya gabatar bai dace ba, sabo da hakan ya saba wa gaskiya.

A hakika, yana kallon ci gaban kasar Sin da girman kai da son zuciya. Bayan karanta makalar, ina ganin dole ne a yi bayani kan ainihin yanayin da ake ciki a kasar Sin don daidaita kurakuran da aka yi, wadanda suka hada da:

Na farko, yin amfani da “ma’aunin waje” wajen auna aikin kasar Sin, shi kan sa wauta ce marar dacewa da yanayin kasar. Makalar ta dogara da ma’auni guda na Bankin Duniya na “dala 8.3 a kowace rana” ga kasashe masu matsakaicin kudin shiga, ba tare da la’akari da yanayin ci gaban kasar Sin da ainihin bukatun jama’arta ba.

ADVERTISEMENT

Yaki da talauci a kasar Sin, ba ya nufin cimma burin samun wani adadi na kuɗin shiga, maimakon haka ya dogara ne a kan biyan bukatun jama’a, inda gwamnatin kasar ta yi kokarin magance damuwar al’umma ta fannonin abinci da tufafi, tare da tabbatar da rayuwarsu ta fannonin samun ilimi na tilas, kiwon lafiya da kuma samun ingantattun gidajen kwana da ruwan sha.

Har ila yau, idan aka kwatanta karfin al’umma na sayen abubuwa, ainihin ma’aunin kawar da talauci na kasar Sin tuni ya zarce ma’aunin talauci na Bankin Duniya.

LABARAI MASU NASABA

Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

Na biyu, makalar ta mai da hankali a kan matsalolin farko da aka fuskanta ga mutanen da suka kaura daga karkara zuwa sabbin wuraren zama da aka gina musu, tana cewa wadanda suka kaura suna fuskantar “matsalar samun aikin yi da kudin shiga”, amma ta yi fatali da ci gaban aikin saukaka fatara da ake yi a kasar. Misali a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar da makalar ta ambata, a tsakanin shekaru biyar da suka wuce, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, kaso 96.2% na mutanen da suka kaura sun samu aikin yi, kuma kudin shigar da suka samu ma ya karu daga yuan 11,228 a shekarar 2020 zuwa yuan 16,927 a shekarar 2024, adadin da ya karu da sama da kaso 50%.

Na uku, a maimakon makalar ta yi nazari a kan matakan da kasar Sin ta dauka na magance komawa talauci, sai ta mai da hankali a kan tasirin annobar COVID-19 da koma bayan tattalin arziki suka haifar, tana cewa akwai yiwuwar “komawa talauci” ga mutane da dama.

Amma a hakika, kasar Sin ta kafa tsarin sa ido da samar da taimako na musamman don magance matsalar komawa talauci ga al’ummar da aka fitar da su daga kangin talauci. Wannan tsari yana shafar dukkanin al’ummun kasar, wanda ke kokarin gano wadanda ke cikin hadarin komawa talauci, don samar da taimako da wuri.

Har zuwa karshen shekarar 2025, an taimaka wa fiye da mutane miliyan 700 a kasar da ake sanya ido don kawar da hadarin komawarsu talauci.

Na hudu, yadda aka tantance gaba dayan aikin da kasar Sin ta yi wajen kawar da talauci bisa wasu al’amura kalilan, ya nuna son zuciya mai zurfi wajen kallon kasar Sin. Ba za a iya musunta cewa, saboda wasu dalilai da ba za a iya kaucewa ba kamar bala’o’i, ko cututtuka masu tsanani, wasu magidanta kalilan na iya fuskantar matsalolin rayuwa na dan lokaci, wannan al’amari ne da kowace kasa ka iya fuskanta a yayin ci gabanta.

Sai dai bai dace ba a fadada wadannan kananan matsaloli, da daukar su a matsayin misali don musanta nasarar kasar Sin wajen yaki da talauci.Kawar da talauci aiki ne mai wuya ga akasarin kasashen duniya. In an duba, ko a Amurka ma kaso 42% na magidantan kasar ba su kai ga samun mafi karancin kudin da ake bukata don rayuwa ba. Sai kuma a Birtaniya, inda jaridar Financial Times take, kimanin mutane miliyan 14.2 suna rayuwa cikin talauci, wanda ya kai fiye da kashi 20% na yawan jama’ar kasar.

Kana a kasar Sin, fitar da al’umma daga kangin talauci ba shi ne karshen aikin rage talauci ba. Don fahimtar abin al’ajabi na rage talauci na kasar Sin, bai kamata a yi watsi da gaba dayan nasarorin da kasar ta cimma ba, sabo da wasu al’amura kalilan da suka faru, haka kuma bai kamata a gurbata gaskiyar yanayin da ake ciki a kasar da kuma shafa mata bakin fenti bisa son zuciya ba.

Duk wani zargi da aka yi bisa son zuciya, ba zai iya dakushe babban aikin yaki da talauci na kasar Sin ba, kuma ba zai iya hana wannan abin al’ajabi ya haskaka tarihin rage talauci na dan adam ba.

CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Taron Intanet Na Sin Karo Na 25 Ya Bayyana Yadda Ake Amfani Da Fasahar AI A Rayuwar Yau Da Kullum
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Tunanin Xi Jinping kan JKS: Hikimar Mulki Ta Farfado Da Kasa Da Kuma Tasirinta A Duniya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin
  • Sulaiman
    Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni
  • Sulaiman
    ‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda
  • Sulaiman
    Taron Intanet Na Sin Karo Na 25 Ya Bayyana Yadda Ake Amfani Da Fasahar AI A Rayuwar Yau Da Kullum

MASU ALAKA

Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin
Daga Birnin Sin

Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

July 9, 2026

Next Post
Adadin Jirage Mara Matuka Masu Rajista Na Kasar Sin Ya Karu Da Kaso 51 A 2025

Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Hukumomin Tsaro

Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Hukumomin Tsaro

July 9, 2026
Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Kasar Sin Na Kara Samun Tagomashi A Kasuwannin Duniya

Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Kasar Sin Na Kara Samun Tagomashi A Kasuwannin Duniya

July 9, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

July 9, 2026
An Gabatar Da Shirin Fadar Potala Ta Kafar CMG

An Gabatar Da Shirin Fadar Potala Ta Kafar CMG

July 9, 2026
kebbi

Makarantu Za Su Ci Gaba Da Zama A Rufe Har Sai Yanayin Tsaro Ya Inganta – Gwamnatin Kebbi

July 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.