Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa ’yan bindigar da suka ƙi zaman lafiya tare da ci gaba da barazana ga rayukan jama’a, musamman a jihar Zamfara dole ne su fuskanci hukunci bisa tanadin doka, babu maganar sulhu da su.
Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a yayin da Gwamnatin Jihar Zamfara ta karɓi baƙuncin wani taron tsaro na musamman kan Arewa maso Yamma, wanda Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta shirya, kuma aka fara gudanar da shi ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau.
An shirya taron na tsawon kwanaki uku ne da taken “Nazarin Ƙalubalen Tsaro a Yankin Arewa maso Yamma”, tare da halartar Babban Sufeto Janar na ’Yansandan Nijeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu.
Mai Magana da Yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris a sanarwar da ya fitar ranar Laraba 19 ga watan Agusta, ya kara da cewa, taron ya haɗa manyan jami’an Rundunar ’Yansandan Nijeriya, wakilan gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma, shugabannin hukumomin tsaro da leƙen asiri, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin fararen hula.
Da yake buɗe taron, Gwamna Lawal ya yaba wa Sufeto Janar na ’Yansanda da shugabancin Rundunar ’Yansandan Nijeriya bisa shirya taron da kuma zaɓar Zamfara a matsayin jihar da za ta karɓi baƙuncinsa.
Ya ce, zaɓar Zamfara na da muhimmanci saboda jihar na ɗaya daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi tsanani a Arewa maso Yamma.A cewarsa, wannan ya sa jihar ta dace da gudanar da cikakken nazari kan matsalolin tsaro da kuma samar da hanyoyin magance su.
Lawal ya ce, matsalar tsaro a yankin ba ta tsaya kan aikata laifuka na yau da kullum ba, domin ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna gudanar da garkuwa da mutane da satar shanu a tsakanin iyakokin jihohi.
Ya ce, hakan na barazana ga rayuwar jama’a, samar da abinci, ilimi, zuba jari da zaman lafiyar al’umma.Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa akwai wasu barazanar tsaro a birane, ciki har da ta’addancin ’yan daba, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kutsen masu tsattsauran ra’ayi.
A cewarsa, irin wannan yanayi na buƙatar a daina amfani da martanin tsaro da ya rabu-rabu, domin masu aikata laifuka ba sa kallon iyakokin jihohi. “Dole tsarin tsaronmu ya kasance haɗe wuri guda. Bayanan sirri daga Zamfara na iya hana hari a wata jiha, haka kuma ayyukan tsaro a makwabciyar jiha na iya daƙile barazanar da ke fuskantar Zamfara,” in ji shi.
A nasa jawabin, Sufeto Janar na ’Yansandan Nijeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya ce tabbatar da tsaron Arewa maso Yamma alhakin kowa ne, saboda muhimmancin yankin ga Nijeriya.
Ya ce hukumomin tsaro sun haɗa ƙarfi tsakanin jihohi domin tunkarar matsalar rashin tsaro, tare da yin sintiri tare da musayar bayanan sirri.
Disu ya ce rundunar ta yanke shawarar kai farmaki ga masu aikata laifuka maimakon ci gaba da jiran hare-harensu.














