ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kaduna: Uba Sani Ya Kashe Sama Da N896m Kan Jin Dadin Malaman KASU

by Sulaiman
3 weeks ago
Ruwa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani ta kashe sama da Naira miliyan 896 wajen kula da jin dadin ma’aikatan Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Babban Sakataren Gwamna na musamman, Farfesa Bello Ayuba, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Laraba, kan wa’adin makonni biyu da kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen KASU ta bai wa gwamnati kafin ta dauki matakin yajin aiki.

Ayuba ya ce ma’aikatan ilimi 59 ne suka bar KASU tun daga watan Janairun 2024 zuwa yanzu, ba 200 ba kamar yadda reshen ASUU-KASU ya yi ikirari.Ya bayyana cewa, ba dukkan ma’aikatan da suka bar jami’ar ne, suka barta sabida rashin kyawun yanayin aiki ba.

ADVERTISEMENT

Ayuba ya ce, “Yana da kyau ku sani cewa daga watan Janairun 2024 zuwa yanzu, ma’aikatan ilimi 59 ne suka bar jami’ar. Daga cikinsu akwai Farfesoshi da Mataimakan Farfesoshi 17 da suka bar jami’ar bisa radin kansu ko kuma suka sauya wurin aiki.

“Cikin bayanai dalla-dalla, Farfesoshi biyu ne suka bar jami’ar a wannan lokacin, da Mataimakan Farfesoshi biyu, manyan Malamai shida, Malamai masu matsayi na 1 guda 10, matsayi na 2 guda 15, sannan akwai mataimakan malmai guda 12 kowanne su”

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Ya kara da cewa sauye-sauyen ma’aikata abu ne da ake samu a jami’o’i saboda yanayin ci gabansu, musamman yadda ake kafa sabbin jami’o’i da kuma samun damar karin matsayi da ke zuwa da su, wanda ke jawo ma’aikata masu mukamai daban-daban.

Ya ce ritayar ma’aikata, da kuma kammala wa’adin ayyukan wucin gadi, ziyara, hutun karatu (sabbatical) da samun kwangiloli, duk suna cikin abubuwan da ke haddasa barin aiki a jami’o’i.

Ayuba ya ce, “Kiran duk irin wadannan sauye-sauyen da ake samu a hukumance da cewa sun faru ne saboda rashin kyawun yanayin aiki, ba tare da gabatar da sahihan bayanai kan dalilan ficewar ma’aikatan ba, babban bata suna ne wanda bai dace da mutanen da ke son ganin an kyautata wurin aikinsu ba.”

Game da jin dadin ma’aikata kuwa, Ayuba ya ce gwamnatin Uba Sani ta ci gaba da nuna jajircewa wajen inganta jin dadin ma’aikatan jami’ar.

Ya ce, “Gwamnatin Uba Sani ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da jin dadin ma’aikata. Ya zuwa yanzu, an kashe sama da Naira miliyan 896 wajen jin dadin ma’aikatan jami’ar.”

KASU
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Next Post
Ku Zaɓi ’Yan Takara Bisa Ayyukansu, Ba Addini Ba — Daurawa

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.