ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bakar Inuwa, Gwamma Rana Da Ke

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 months ago
Bakar inuwa

Su wane ne abokai na jabu? Wato wadanda maimakon su ba ka taimako, sai su nemi haifar maka da karin matsaloli.

Sanin kowa ne, aboki na gaske har kullum yana son ba ka taimako. Misali, a kwanan baya, kasar Sin ta sanar da fara soke dukkan harajin kwastam da ta saka ma kayayyakin kasashe 53 dake nahiyar Afirka, wadanda suka kulla huldar diflomasiyya da ita, ciki har da Najeriya, tun daga ranar 1 ga watan Mayun dake tafe. Wannan manufa za ta taimaki kasashen Afirka wajen fitar da karin kayayyaki zuwa kasar Sin, da raya masana’antu a gidajensu. Ta hanyar rage ribar da ita kanta za ta samu, kasar Sin na neman samar wa abokan hulda karin damammakin raya kasa. Hakan ya nuna niyyar kasar ta zama wata abokiya mai cikakken sahihanci.

Sai dai mene ne abun da kasar Amurka take yi a lokaci daya? A kwanan baya, majalissar wakilai ta kasar Amurka ta fara tantance wani daftarin kundin doka da ya shafi batun ’yancin bin addini a kasar Najeriya. Cikin kundin, an ci gaba da kururuta batun “cin zarafin mutane masu bin addinin Kirista a Najeriya” da na “ayyukan ta’addanci da dakaru ’yan kabilar Fulani suke yi”, kuma an ce wai “Sinawa suna haka ma’adinai ba bisa doka ba a Najeriya, da biyan kudi ga Fulani ’yan bindiga don samun izinin yin haka”. Dangane da zargin da kasar Amurka ta yi, Charles Onunaiju, wani shehun malami mai nazarin harkokin kasar Sin, ya rubuta wani bayanin da aka wallafa shi a jaridar “The Nation” ta Najeriya, inda ya ce kasar Amurka tana shafa wa bangaren Najeriya kashin kaza, tare da neman haddasa husuma tsakanin kasashen Najeriya da Sin.

ADVERTISEMENT

Hakika tuni gwamnatin Najeriya ta kare kanta daga zargin da kasar Amurka ta yi mata, inda ta ce, hare-hare da ayyukan ta’addanci da ake samu a wasu yankunan kasar ba su da alaka da batun addini, kana bai kamata a dora wa wata kabila laifin ta’addanci ba. Kana a nata bangare, kasar Sin ita ma ta yi watsi da zargin da kasar Amurka ta yi, inda ta ce kamfanonin sarrafa ma’adanai na kasar Sin suna kokarin bin dokokin kasar Najeriya, yayin da suke gudanar da ayyukansu a kasar.

Sai dai me ya sa kasar Amurka ke son shafa wa Najeriya da Sin bakin fenti? A cewar Charles Onunaiju, tun daga shekarar 2025, an riga an kaddamar da dimbin masana’antun sarrafa Lithium a kasar Najeriya, wadanda wasu kamfanonin kasar Sin suka zuba musu jari. Batun na alamta cewa, kasar Najeriya za ta sauya daga fitar da danyen sinadari zuwa harkar sarrafa ma’adini don daga darajarsa, ta fuskar aikin raya masana’antun Lithium, da kara taka muhimmiyar rawa a tsarin samar da baturan motoci na duniya. Sai dai a nata bangare, kasar Amurka na kallon Najeriya a matsayin yankin dake karkashin kulawarta, don haka ba ta son ganin yadda kasar Sin ta haifar da karin tasiri kan Najeriya, ko da yake tasiri ne da zai ba Najeriya damammakin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Abun da kasar Amurka take yi shi ne, fakewa da zargin da ta yi wa kasashen Najeriya da Sin, don neman rusa alakar dake tsakanin kasashen biyu, duk da cewa hakan zai lalata makomar kasar Najeriya.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Kamar yadda wani mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook dan Najeriya mai suna Phils ya fada, “Idan kana tsammanin Amurkawa na kaunar ’yan Najeriya masu bin addinin Krista, to, ni dai na tabbata, wannan ‘kauna’ ta shafi niyyar kare moriyar kasar Amurka ce kawai.”

Batun nan ya tunatar da ni da wani karin magana, wato “Bakar inuwa, gwamma rana da ke.” (Bello Wang)

Bakar inuwa
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Bakar inuwa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara
  • Sulaiman
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Sulaiman
    Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Sojoji Sun Sake Ceto ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 5, Sun Ceto Yara 3 A Borno Da Yobe

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.