Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta kammala ɗaukar manyan ‘yan wasa biyu, Rodri da João Cancelo, a matsayin wani ɓangare na shirinta na ƙarfafa tawagar kafin sabuwar kakar wasa. Barcelona ta ɗauki Rodri daga Manchester City kan kuɗin Yuro miliyan 75, yayin da Cancelo ya koma ƙungiyar ba tare da an biya kuɗin cinikinsa ba.
Barcelona ta daɗe tana zawarcin Rodri, wanda daga ƙarshe ya yanke shawarar komawa Camp Nou bayan yunƙurinsa na komawa Real Madrid ya ci tura. Rodri ya zama ɗan wasa na huɗu da Barcelona ta ɗauka a wannan kakar, bayan Karim Adeyemi, da Anthony Gordon da João Cancelo.
A wani ɓangare kuma, Barcelona ta rabu da ɗan wasanta na gaba, Ferran Torres, wanda ya koma Paris Saint-Germain (PSG) kan kwantiragin shekaru huɗu. PSG ta biya Yuro miliyan 50 domin kammala cinikin ɗan wasan.
Barcelona na fatan sabbin ‘yan wasan za su taimaka mata wajen ci gaba da samun nasarori a sabuwar kakar, bayan da ƙungiyar ta lashe gasar La Liga a kakar wasan da ta gabata.














