Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), mai mulki a Jihar Bauchi, ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi, inda take ƙalubalantar cancantar Sanata Shehu Buba Umar na tsayawa takarar gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP).
Jam’iyyar ta nemi kotun da ta duba shiga cikin PRP da kuma lashe zaɓen fitar da gwani na neman tikitin gwamna a ƙarƙashin PRP ko sun yi daidai da tanade-tanaden sashe na 77(4), 77(5) da 77(6) na Dokar Zaɓe ta 2026 ko akasin haka.
Mai ba da shawara kan harƙoƙin shari’a na APM, Barista Jidauna Tula, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ’yan jarida bayani a Bauchi jiya, inda ya ce an shigar da ƙarar ne domin tabbatar da adalci da gaskiya, tare da samun bashin baƙin kotu kan tanade-tanaden dokar zaɓen da abin ya shafa da suka danganci neman gwamna da Shehu Buba ke yi.
Ƙarar mai lamba FHC/BAU/CS/68/2026 ta zayyano hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), jam’iyyar PRP da Sanata Shehu Buba Umar a matsayin waɗanda ake ƙara.
A cewar Barista Tula, APM na ƙalubalantar cancantar Buba ne bisa zargin cewa ya shiga zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kafin daga bisani ya zama ɗan takarar gwamnan Bauchi na PRP.
Ya kuma yi zargin cewa sunan Buba bai kasance cikin rajistar ’yan jam’iyyar PRP da aka miƙa wa INEC a cikin wa’adin da doka ta tanada ba, amma daga baya aka saka sunansa cikin jerin sunayen ’yan takarar da hukumar ta fitar na ƙarshe domin su nemi takarar gwamna a 2027.
A cikin takardar ƙarar da ta gabatar wa kotun, APM ta nemi a tantance ko shiga da Buba ya yi a zaɓen fitar da gwani na takarar gwamnan PRP da aka gudanar ranar 25 ga Mayu, 2026, da kuma tsayar da shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar daga bisani, sun yi daidai da doka.
Jam’iyyar ta kuma nemi kotun ta tantance ko Buba yana da cancantar shiga zaɓen fitar da gwanin, alhali kuwa, a cewar APM, sunansa bai cikin rajistar ’yan jam’iyyar PRP da aka miƙa wa INEC a cikin wa’adin da doka ta tanada ba.
Wani batu da aka gabatar a cikin ƙarar shi ne ko zargin cewa Buba ya ci gaba da kasancewa mamba na APC a lokacin da PRP ta miƙa rajistar mambobinta ga INEC yana da tasiri kan cancantarsa ta shiga zaɓen fitar da gwani na PRP da kuma fitowarsa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
APM ta kuma nemi kotun ta fayyace ko PRP ta bi tanadin sashe na 77(4) na Dokar Zaɓe ta 2026, ta hanyar miƙa rajistar mambobinta ga INEC kafin ko a ranar 10 ga Mayu, 2026, wato kwanaki 15 kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani na takarar gwamna da aka yi ranar 25 ga Mayu, 2026.
Haka kuma, jam’iyyar ta nemi kotun ta fayyace ko PRP za ta iya dogaro da wata rajistar mambobi daban da wadda ta miƙa wa INEC a cikin wa’adin da doka ta tanada domin tabbatar da cancantar Buba ta shiga zaɓen fitar da gwani.
APM na kuma tambayar ko INEC za ta iya ci gaba da riƙe sunan Buba a cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Bauchi na 2027 bisa doka, idan kotu ta gano cewa shiga da ya yi a zaɓen fitar da gwani da kuma tsayar da shi a matsayin ɗan takara sun saɓa wa Dokar Zaɓe.
Saboda haka, APM ta nemi kotun ta ayyana cewa wallafa jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta yi a ranar 10 ga Oktoba, 2026, wanda ya nuna Buba a matsayin ɗan takarar gwamnan Bauchi na PRP, ya saɓa wa doka, kuma ba shi da inganci ko wani tasiri a gaban doka.Ta kuma nemi kotun ta umarci INEC da ta cire sunan Buba daga jerin sunayen ’yan takarar zaɓen gwamnan jihar na 2027.
Da yake bayyana tushen shari’ar da aka shigar, Tula ya ce Sashe na 77(4) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa rajistar mambobinsu ga INEC aƙalla kwanaki 21 kafin ranar da aka tsara gudanar da zaɓen fitar da gwani, tarukan jam’iyya da manyan tarukanta.
Ya ƙara da cewa Sashe na 77(8), kamar yadda aka ambata a cikin ƙarar, ya tanadi cewa mambobin jam’iyya waɗanda sunayensu ke cikin rajistar mambobin da ta dace ne kawai suke da damar kaɗa ƙuri’a ko kuma a zaɓe su a zaɓen fitar da gwani, tarukan jam’iyya da manyan tarukanta.
Tula ya kuma yi hujjar cewa Sashe na 77(6) ya hana jam’iyyun siyasa dogaro da wata rajistar mambobi daban da wadda suka miƙa wa INEC a cikin wa’adin da doka ta tanada domin zaɓen fitar da gwani, tarukan jam’iyya ko manyan tarukanta.
A cewarsa, PRP ta kamata ta miƙa rajistar mambobinta ga INEC kafin ko a ranar 10 ga Mayu, 2026, amma ya yi zargin cewa sunan Buba bai cikin rajistar a lokacin da aka miƙa ta.
Ya kuma yi zargin cewa Buba ya ci gaba da kasancewa mamba na APC har zuwa ranar 19 ga Mayu, 2026, bayan da PRP ta riga ta miƙa rajistar mambobinta ga INEC. A cewarsa, wannan yanayi ya haifar da tambayoyi kan cancantar Buba ta shiga zaɓen fitar da gwani na PRP da aka gudanar ranar 25 ga Mayu, 2026.
APM na da ra’ayin cewa shiga da Buba ya yi a zaɓen fitar da gwani da kuma fitowarsa a matsayin ɗan takarar gwamnan Bauchi na PRP sun saɓa wa tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.
Saboda haka, jam’iyyar ta dage cewa tsayar da Buba a matsayin ɗan takara ya saɓa wa doka kuma ba shi da inganci a gaban doka. Ta kuma nemi kotun ta soke tsayar da shi tare da umartar INEC da ta cire sunansa daga jerin sunayen ’yan takarar zaɓen.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, INEC, PRP da Sanata Shehu Buba Umar ba su mayar da martani kan lamarin ba. Sai dai wakilinmu na ci gaba da ƙoƙarin samun martanin ɓangarorin da abin ya shafa.













