Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Auwal Jatau, ya ƙaddamar da na’urorin ɗaukar hoton ciki na zamani guda 20 masu amfani da fasahar 4D, da kayan daƙile zubar jini guda 73, waɗanda kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 625, domin rarraba su ga manyan da ƙananan asibitoci faɗin jihar.
Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da na’urorin a gidan Gwamnatin jihar Bauchi a ranar Talata, mataimakin Gwamnan ya ce waɗannan kayan aikin za su taimaka sosai wajen kyautata harkokin kiwon lafiyan mata masu juna biyu da yara a jihar.
Ya nanata cewa gwamanti mai ci ta Bala Muhammad ta himmatu wajen sauƙaƙa yanayin samun kiwon lafiya cikin sauƙi da inganci, musamman a bangaren lafiyar mata da yara.
Auwal ya ce da zarar aka inganta kiwon lafiyan mata da yara to an samu sauƙin rage matsaloli da dama a cikin al’umma.
Ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗa kai da ƙungiyoyin agaji da abokan jere domin samun ƙarin tallafi da zai inganta ayyukan kiwon lafiya.
A nasa jawabin, shugaban jukumar Kula da lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi, Dakta Rilwanu Mohammed, ya bayyana cewa an sayo kayan aikin ne a shekarar 2025, amma ba a samu damar rarraba su zuwa cibiyoyin lafiya ba saboda matsalolin jigilar kayayyaki, waɗanda yanzu aka shawo kansu.
Ya ce bayan ƙaddamar da kayan aikin da Mataimakin Gwamnan ya yi, za a rarraba su ga cibiyoyin lafiya nan take domin fara amfani da su.
Shi kuma Dakta Adamu Mohammed, ya ce kayan aikin da aka ƙaddamar wani ɓangare ne na kayayyakin da aka samar ƙarƙashin shirin IMPACT.
Ya ce, “Waɗannan na’urori na daga cikin sabbin na’urorin daukar hoton ciki na zamani da ake da su a duniya.”
A cewarsa, na’urorin suna da ayyuka daban-daban, ciki har da yin gwajin gaggawa na ciki.
Ya ce na’urorin za su taimaka wajen gudanar da gwaje-gwajen mata masu juna biyu domin gano matsayin jariri a cikin mahaifa, adadin jarirai, halin da suke ciki da kuma abun da dace a yi musu domin ganin uwa ta sauƙa lafiya.
Ya ƙara da cewa ana iya amfani da na’urorin wajen yin transvaginal da transabdominal ultrasound, sannan kuma ana iya amfani da su wajen yin echocardiography da Doppler scanning.
Dr. Mohammed ya bayyana cewa kasancewar na’urorin na 4D na ba da damar duba gaɓoɓin jiki daga kusurwoyi daban-daban har zuwa digiri 360, wanda zai taimaka wajen samar da ingantaccen sakamakon bincike da gano cututtuka.
Ya ce an sayi na’urorin ne da tallafin aikin Bankin Duniya, kuma za a rarraba su ga dukkan asibitocin gwamnati na ƙananan hukumomi guda 20 da ke jihar.
A cewarsa, ana sa ran kimanin mata masu juna biyu 30,000 za su amfana da wannan shiri a matsayin wani mataki na gaggawa na inganta lafiyar al’ummar Jihar Bauchi.
Ya bayyana cewa kayan dakile zubar jinin, wato anti-shock garments, wata hanya ce da ake amfani da ita wajen daƙile ci gaba da zubar jini ga mata masu juna biyu.
Ya ce idan mace ta samu matsanancin zubar jini bayan haihuwa (postpartum haemorrhage) a cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko, kuma ma’aikatan lafiya suka gano cewa jinin ya wuce abin da cibiyar za ta iya kula da shi, za su sanya mata kayan daƙile zubar jinin domin dakatar da zubar jinin na wani lokaci da kuma hana ta shiga halin gigicewa sakamakon rashin jini.
Ya ƙara da cewa daga nan za a tura matar tare da kayan daƙile zubar jinin zuwa babban asibiti mafi kusa, inda za ta samu cikakkiyar kulawar da take bukata.














