Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan jami’ai da fasinjojin da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin saman NAF mai lamba NAF 931, kirar ATR 42, a yankin Igbokoda na Jihar Ondo.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, wadda Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na Hedikwatar NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya sanya wa hannu, shugaban rundunar ya bayyana hadarin a matsayin wani lamari mai matukar radadi ga Rundunar Sojin Sama da kasa baki daya.
Aneke ya jajanta wa iyalan, ’yan uwa da abokan aikin wadanda suka mutu, yana mai tabbatar musu da cewa Rundunar Sojin Sama za ta kasance tare da su a wannan lokaci mai wahala.
Sanarwar ta ce jirgin NAF 931 na dauke da mutane 25, wadanda suka hada da ma’aikatan jirgin guda biyar da fasinjoji 20. Jirgin yana gudanar da wata tafiya ta yau da kullum daga Benin zuwa Legas ne lokacin da hadarin ya afku.
Sanarwar ta kara da cewa an fara aikin bincike da ceto nan take, tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa domin gano tare da tantance dukkan mutanen da ke cikin jirgin.
Sai dai NAF ta ce ba a samu wani wanda ya tsira daga hadarin ba.
Shugaban Rundunar Sojin Sama ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hadarin da kuma abubuwan da suka kai ga faruwar lamarin.
Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta ce za ta ci gaba da fitar da sahihan bayanai cikin lokaci yayin da binciken hadarin ke ci gaba.














