Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen matsalar rashin wutar lantarki na tsawon shekaru 17 da ta dabaibaye garin Tallasse da sauran al’ummomin Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, biyo bayan ƙaddamar da aikin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana (solar mini-grid) mai ƙarfin megawatt 1 (1MW) tare da batir mai ɗaukar nauyin kilowatt-hour 2,400 (2.4MWh).
Wannan aiki, wanda Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA) ta aiwatar tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Gombe da wani kamfani mai zaman kansa, an kaddamar da shi ne domin farfaɗo da harkokin yau da kullum da tattalin arziƙin yankin.
A yayin bikin ƙaddamarwar, an kuma bayar da umarnin fara aikin gina cibiyoyin wutar lantarki mai amfani da hasken rana masu ƙarfin megawatt 16 (16MW) da za su haɗa al’ummomin Dukku, da Bajoga, da Kumo, da Kaltungo a jihar. Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, wanda ya bayyana aikin a matsayin wata shaida ta manufar “Sabon Fata” (Renewed Hope Agenda) na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewa gwamnati na faɗaɗa amfani da sabon makamashi a jihohi daban-daban domin kawo wadataccen haske ga al’ummomin karkara.
Aikin wutar lantarkin na garin Tallasse ya riga ya fara samar da wuta ga gidaje da cibiyoyin sana’o’i sama da 6,028, kuma aikin ya ƙunshi injinan sarrafa gyaɗa domin fitar da mai, injinan niƙa shinkafa da fulawa masu amfani da wutar lantarki, gami da adaidaita-sahu (Keke NAPEP) masu amfani da batir. Masana da jami’an gwamnati sun bayyana cewa wannan tsari zai sauya fasalin tattalin arziƙin yankin na Balanga wanda ya shahara a fannin noma, ta hanyar sauƙaƙa sarrafa amfanin gona da rage dogaro da man fetur a maimakon takaita amfanin wutar ga hasken kwan-fitila kaɗai.
A nasa jawabin, Babban Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar REA, Abba Aliyu, ya bayyana cewa hukumar ta sauya akalarta daga ƙididdige yawan wutar da aka kafa zuwa auna ainihin ci gaban da ayyukan ke haifarwa ga rayuwar al’umma. Ya fayyace cewa an gudanar da aikin ne a ƙarƙashin shirin faɗaɗa samar da makamashi (DARES), tare da sanya na’urorin zamani masu sa-ido da kuma tsarin aiki mai ɗorewa domin tabbatar da cewa an samar da wutar da za ta ɗore ba tare da fuskantar cikas ba.
A ƙarshe, Shugaban Ƙaramar Hukumar Balanga, Ibrahim Salihu, ya nuna gagarumar godiyarsa ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Gombe bisa wannan aiki, inda ya buƙaci al’ummar yankin da su kiyaye kayayyakin wutar daga ɓarnatawa. Ya kuma buƙaci manoma, da ƴan kasuwa, da matasa da su yi kyakkyawan amfani da wannan haske domin bunƙasa sana’o’i, da inganta ilimi, da haɓaka ayyukan asibitoci da sauran hanyoyin dogaro da kai.














