Tun daga matakan katse samar da sassan laturoni na chip, zuwa hana shigar da wasu kayayyakin fasaha, salon wani ya samu saura su rasa, na ingiza faduwar Amurka a fannin babakeren fasahohi.
A baya-bayan nan, Amurka ta nuna damuwa mai alaka da “Tsaron Kasa”, tare da bayyana shirinta na kakaba wasu shingaye, da takunkumai kan kamfanonin Sin na fasahar AI, tare da kara matse damar shigar da hajoji masu alaka da fasahohin zamani cikin kasar.
Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta Sin ta gudanar, tsakanin masu amfani da intanet na kasa da kasa, ya nuna kaso 83.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na nuna damuwa, game da yiwuwar Amurka ta sauya matsaya, daga mai yayata bude kofar cin gajiyar fasahohi zuwa mai bayar da kariyar cinikayya a fannin, suna masu ganin cewa daukar wannan mataki, na iya gurgunta ayyukan bincike, da amfani da fasahohin AI na duniya.
Kazalika, kaso 89.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu, cewa manhajojin AI za su bunkasa ne kadai, idan an bude damar cin gajiyarsu ga kowa da kowa, kana an ci gaba da ingantawa, da tace su ta hanyar sauraron bahasi daga masu amfani da su na sassa daban daban.
To sai dai kuma, gwamnatin Amurka ta ci gaba da tsaurara matakai kan budaddun hajojin AI na kamfanonin kasar Sin. Don gane da hakan, kaso 89.7 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi kira da a warware dukkanin sabani, masu nasaba da ikon mallakar fasahohin AI ta hanyar ka’idojin kasa da kasa, maimakon yawaita daukar matsayar kashin kai a kowace gaba. (Saminu Alhassan)













