A yau Alhamis 30 ga watan nan na Yuli ne aka bude bikin nune-nunen yayata al’adun gado wadanda ba na kayayaki ba, mai lakabin “Xinjiang, a Wonderful Land”, na shekarar 2026 a birnin Shihezi na jihar Xinjiang.
Taron, wanda ya gudana bisa goyon bayan gwamnatin jihar ta Xinjiang, ya hallara ayyukan wakilcin al’adun gado wadanda ba na kayayyaki ba har 651, da magadan irin wadannan ayyuka har 549 daga sassa daban daban na kasar Sin.
Kazalika, taron ya shaida tsarin gudanar da nune-nune na hadaka, da hadin gwiwar samarwa, da raba gajiya, inda magadan irin wadannan ayyuka suka yi ayyuka tare don gabatar da ayyukan al’adun gado wadanda ba na kayayyaki ba, da dandalolin horarwa a fannin, inda suka samar da wani tsari na hadin kai don koyi da juna, da musaya a tsakaninsu tare da gabatar da kawance na hakika tare. (Saminu Alhassan)













