Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Bitirhuya da ke ƙaramar hukumar Hong a Jihar Adamawa, inda suka kashe mutane huɗu tare da ƙone gidaje da dama.
Rahotanni sun ce maharan sun shiga garin a kan babura da misalin tsakanin ƙarfe 5 zuwa 6 na yammacin ranar Lahadi, suna harbe-harbe yayin da mazauna garin suka tsere domin tsira da rayukansu.
Mutane huɗu ne aka kashe yayin harin.
Harin ya faru ne ƙasa da mako guda bayan da ’yan ta’addan suka kashe mutane 12 a ƙauyen Nzangola da ke ƙaramar hukumar Gombi.
Shugaban ƙaramar hukumar Hong, Aliyu Sa’ad Yerima, ya tabbatar da faruwar harin yayin da ya kai ziyara garin.
Ya jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe tare da alƙawarin ƙara ƙoƙarin inganta tsaro.
Ya buƙaci mazauna yankin su riƙa kai rahoton mutanen da suke zargi ga jami’an tsaro, tare da gargaɗin duk wanda ke taimaka wa ko haɗa kai da ’yan ta’adda zai fuskanci hukunci.
Mazauna yankin sun roƙi Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Adamawa da su ƙara ɗaukar matakan tsaro domin kare al’ummomin karkara daga hare-hare.













