Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayar da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa da ke Mabera, bayan da wani matashi ya caka masa wuƙa jim kaɗan bayan idar da Sallar Juma’a a makon da ya gabata.
Gwamnatin ta kuma umarci a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin, tare da ayyana masallacin a matsayin wurin da ake gudanar da binciken manyan laifuka har sai an fitar da sabon umarni.
Rahotanni sun ce wani matashi da ke cikin masu salla ya kai wa Sheikh Lukuwa hari da wuƙa jim kaɗan bayan idar da Sallar Juma’a.
An ce matashin ya yi masa rauni a wuya da hannun hagu.
Sauran masu masallata sun cafke wanda ake zargin, inda suka lakaɗa masa dukan da ya yi sanadin ajalinsa kafin jami’an tsaro su isa wajen.
’Yansanda sun tabbatar da cewa mutum ɗaya ya rasu sakamakon rikicin.
An garzaya da Sheikh Lukuwa zuwa asibiti domin kula da shi.
Daga baya, kakakin ’yansandan jihar, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce an sallame shi bayan likitoci sun kula da lafiyarsa.
Shi ma malamin ya bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya tare da kira ga mabiyansa da jama’a su kwantar da hankalinsu.
Lamarin ya haifar da tashin hankali a wasu sassan birnin Sakkwato, ciki har da Sahara, Bello Way da Aliyu Jodi.
Wasu ’yan kasuwa sun rufe shaguna na ɗan lokaci saboda fargabar ɓarkewar rikici, yayin da jami’an tsaro suka mamaye muhimman wurare domin tabbatar da zaman lafiya.
Wasu rahotanni sun danganta harin da wata tsohuwar magana da Sheikh Lukuwa ya yi a wani wa’azinsa, wadda ta jawo ce-ce-ku-ce da barazana a baya.
An kuma ruwaito cewa malamin da wasu mabiyansa sun kai ƙorafi ga gwamnatin jihar kwanaki kaɗan kafin harin, inda suka nuna damuwa kan barazanar da suke fuskanta.
Sai dai ’yansanda suna bincike domin gano ainihin abin da ya jawo harin.
’Yansanda sun yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da barin hukumomi su gudanar da bincike a kan lamarin.














