Rundunar ’yansandan Nijeriya ta sanya jami’anta a faɗin ƙasar cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon bayanan sirri kan yiwuwar hare-haren ta’addanci.
Rundunar ta ce wuraren da ake zargin ’yan ta’addan za su iya kai wa hari sun haɗa da wuraren ibada, makarantu, sansanonin masu yi wa ƙasa hidimi (NYSC) da sauran wuraren taruwar jama’a.
Bayanan sirrin sun kuma nuna cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai daga Jihar Katsina, Kaduna sun nufi zuwa Jihar Filato.
Bayan samun wannan rahoto, babban kwamandan ’yansanda ya umarci rundunonin ’yansanda a faɗin ƙasar da su ƙara tsaurara matakan tsaro tare da hana miyagun ƙungiyoyin aiwatar da shirinsu.
Rahotanni sun ce an fitar da sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 13 ga watan Satumba 2026, wanda aka aike wa shiyyoyin ’yansanda, rundunoni na musamman da kwamishinonin ’yansanda na jihohi 36 da Abuja.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a samu ƙarin bayani daga kakakin rundunar ’yansandan Nijeriya, CSP Ani Iniedu, ba.














