ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bude Kofa Ta Kowace Fuska Wata Hanya Ce Ta Samun Makoma Ta Bai Daya

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago

Da misalin karfe 5:13 na sanyin safiyar jiya Litinin, ’yan sama jannatin Shenzhou 21 suka bude kofar tashar binciken sararin samaniya ta Sin, domin maraba da ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-23, wannan shi ne karo na 8 da ’yan sama jannatin kasar Sin suka hadu a sararin samaniya.

Wani babban batu shi ne yadda a karon farko, ’yar sama jannati daga yankin Hong Kong na Sin watau Li Jiaying, da ake kira Lai Ka-ying, ta shiga tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin.A ganina, wannan gagarumin lamarin da ya watsa wa masu bata sunan kasar Sin kasa a ido, domin ya tabbatar da manufar nan ta “kasa daya mai tsarin mulkin biyu.” Duk da cewa yankin Hong Kong na kasar Sin, yanki ne na musamman mai cin gashin kansa, to yana karkashin babban yankin Sin, kuma Sin na shigar da shi cikin harkokin da suka shafi ci gaban kasa da na al’umma domin samun moriya da makoma ta bai daya ba tare da mayar da wane bangare saniyar ware ba.

Yadda matashiya daga yankin ta shiga cikin aikin na sama jannati, ya sake tabbatar da burin al’ummar Sinawa na ganin dunkulewar kasarsu wuri guda, ya tabbatar cewa, masu neman ta da zaune tsaye ne ke ingiza ’yan aware. Baya ga ’yar sama jannati daga yankin Hong Kong, a ranar 22 ga watan Afrilun bana, kasar Sin ta sanar da cewa an zabi wasu ’yan kasar Pakistan biyu a matsayin ’yan sama jannati na kasar waje na farko, da za su karbi horo domin shiga aikin binciken samaniya na Sin.

ADVERTISEMENT

An ce Muhammad Zeeshan Ali da Khurram Daud, za su karbi horo a kasar Sin, kuma bayan sun kammala horo da tantancewa, daya daga cikinsu zai shiga cikin tawagar masu aikin binciken samaniya na Sin, inda zai zama dan sama jannati na farko na kasar waje da zai shiga tashar Tiangong ta kasar Sin.

Watau wannan ya kara bayyana ma’anar manufar bude kofa ta Sin, inda yake nuna cewa, ba kawai ga kasuwanci ko bude ido kasar Sin ke bude kofarta ba, tana budewa ne ta kowane bangare domin samun ci gaba na bai daya.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Hakika wannan na zaman gagarumar nasarar hadin gwiwar kasa da kasa a fannin binciken samaniya ta Sin. Wannan ya tuna min da wata ’yar Nijeriya, Dr. Olusola Ashiru wadda kasar Sin ta ba ta damar shiga aikin nutso domin bincike a karkashin teku a shekarar 2024. Kafin sannan ta ce ba ta taba samun wannan dama ba, inda take dogoro da ayyukan wasu wajen koyar da dalibanta.

Dukkan wadannan yunkuri na kasar Sin na kara bayyana ra’ayi da kuduri da burinta na bude kofa da musayar ilimi da hadin gwiwa domin samun moriyar juna.

Bisa gayyatar karin bangarori da kasashe domin hadin gwiwar gudanar da binciken kimiyya, za a gaggauta samun ilimi da fahimtar abubuwa masu sarkakiya da inganta kare duniya da kuma samun ci gaba da moriya na bai daya, wandanda za su kai ga samar da al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Fa’iza Mustapha)

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi
  • Sulaiman
    Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
  • Sulaiman
    An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu
  • Sulaiman
    Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

MASU ALAKA

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi
Daga Birnin Sin

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT
Daga Birnin Sin

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin
Daga Birnin Sin

Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

September 12, 2026
Next Post
Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 1

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
jam'iyyu

An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu

September 12, 2026
Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

September 12, 2026
Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

September 12, 2026
2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.