ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bude Kofar Kasar Sin Turba Ce Ta Hadin Kan Duniya

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago

Fadada bude kofa da kasar Sin ke ci gaba da yi ga duniya wata turba ce ta samun bukasar kasuwanci da daidaiton tsarin samar da kayayyaki a duniya.

Amma a karkashin wannan, akwai wata muhimmiyar alkibla da ta cancanci a lura da ita, watau rawar da kasar ke takawa a matsayin wata cibiyar hadin kai ta dogon lokaci tsakanin kasashe, wadda ta ginu kan tabbaci, fadada fasaha, da hadin gwiwar manyan yankuna daban-daban na duniya.

Akwai masharhanta da dama da suka jaddada gudunmawar Sin ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da kuma muhimmiyar ma’anar da take dauke da ita, sakamakon yadda tsarin ci gaban Sin yake ba sauran kasashe damar shigo da kayayyaki kawai ba, har ma da shiga cikin tsarin masana’antunta mai kwari domin cin gajiyar bude kofarta.

ADVERTISEMENT

Wannan tsari wanda yake samun tagomashi ba tare da tangarda ba bisa ingantattun ababen more rayuwa da kayayyakin aiki, da kuma ci gaba mai dorewa a bangaren samar da kayayyaki, yana bai wa abokan hulda tabbaci mai karfi a lokacin da kasuwannin duniya ke fuskantar rashin tabbas.

Daga wannan, ana iya kara fahimtar cewa fadada bude kofar Sin ba wai kawai damar shiga kasuwarta ba ce, amma dama ce ta shiga cikin wani cikakken tsarin samun ci gaba mai alfanu bisa kyawawan manufofi da tsare-tsare masu hangen nesa wadanda suke kara fayyace kasar Sin a matsayin wacce ta zarce zama cibiyar masana’antu kawai zuwa wani tsarin da ya hada da kirkira da kuma bincike.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Don haka duk kamfanoni ko daidaikun masu zuba jari a kasar a karkashin manufarta ta fadada bude kofa, ba kawai masu saka jari ne ba, har ma abokai ne na gudanar da huldar samun nasara ga kowane bangare.Kazalika, wani sashe da bude kofar kasar Sin ke muhimmantawa shi ne karfafa hadin kai da cin moriya tare maimakon gasa mara tsabta da gitta shingen cinikayya.

Kamar yadda wani mai fashin baki kan tattalin arziki daga yankin Turai, Patrick Hollenfeltz ya taba bayyanawa, yin hadin gwiwa tsakanin karfin samar da kayayyaki na kasar Sin da kuma ingataccen tsari da fasahar yankin Turai ba kawai yana da alfanu ga ci gaban tattalin arzikin sassan biyu ba ne, har ma zai taka rawar gani wajen sauya rikice-rikice da rashin tabbas a duniya zuwa hadin gwiwa mai amfanar da kowa.

A takaice dai, bayan gudunmawar da bude kofar kasar Sin ke bayarwa ga tabbatar daidaita tsarin samar da kayayyaki a duniya, har ila yau, lamarin yana taimakawa wajen dunkulewar tattalin arzikin duniya ta hanyar karfafa hadin gwiwa, da samar da kwarewa da cin gajiya tare da saura, da kuma tabbatar da kyakkyawan tsari na ci gaba mai dorewa a duniya. (AbdulrazaqYahuza Jere)

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Zamfara

Jami'an Tsaro Na Zamfara Sun Cafke Mota Ɗauke da Abubuwa Masu Fashewa 98 Zuwa Sansanin ‘Yan Bindiga

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.