ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

by Bello Hamza
2 months ago
Arewa

A makon jiya ne Editanmu Bello Hamza ya tattauna da Alfa Ahmad Musa wani matashi da ya yi watsi da fafutukar neman aikin gwamnati duk da yana da digiri biyu a makatun boko. Maimakon neman aikin gwamanti ya kafa kamfani nasa na kansa, inda ya kirkiro da manhajar da za ta taimaka wa ‘yan kasuwa gudanar da harkokin su cikin aminci. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Da farko za mu so ka gabatar da kanka

Sunana Alfa Ahmad Musa mazaunin Legas amma haifaffen Zariya ne, na yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello na karanta ‘Computer Science’, sannan na je mataki na gaba inda na yi digree na biyu a kan ‘Project Management da System Thinking’ da kuma ‘System Analysis’, bayan haka yanzu ina da cikakken kwarewa a kan ‘Network Defence’ da kuma ‘Serber Security’, da wannan ilimin ne na yanke shawarar kafa kamfanin da zai taimaki mutanenmu na Arewa.

ADVERTISEMENT

Kwanan nan kuka gabatar da wani gagarumin taro wanda kuka kira ‘yan kasuwa don fadakar da su kan hanyoyin yin kasuwanci ta kafofin sadarwa na zamani, ya taron ya kasance?

Alhamdu lillahi, taro ne gagarumi da muka gayyaci ‘yan kasuwa da yawa da ke Zariya da kewaye sannan kuma muka gayyaci masana wadanda suka dade a harkar, suka zo suka ba su shawarwari suka gaya musu yadda kasuwanci ya kamata ya kansace a wannan zamanin. Sannan mun kuma gabatar musu da manhajar mu ta SAYARWA wanda amfani da shi zai taimaka musu sosai wajen gudanar da harkokin kasuwancin su.

LABARAI MASU NASABA

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

2027: Shugaba Mai Gaskiya Da Hangen Nesa Nijeriya Ke Buƙata —Ahmad Shu’aibu

To yaya martanin matasa ‘yan kasuwa na Zariya?

Wato mun ga martani sosai, na jin dadi daga wurin matasa, ba ma matasa kadai ba har ma wakilan kungiyoyin ‘yan kasuwa sun nuna mana jin dadinsu saboda mun fadakar da su sosai, masana sun fadakar da su sosai kan abubuwa da dama, an kuma fadakar da su a kan bukatar Sanya gaskiya da rikon amana a yayin gabatar da kasuwancin su.

To wane kira kake da shi ga gwamnati da al’umma da masu hannu da shuni wajen ganin an bunkasa ilimin matasa a wannan bangare?

Wato kiran da nake da shi ga gwamnati da mutane da masu hannu da shuni shi ne, ya kamata a ce yanzu mun gane cewa, lokaci ya yi da za mu rika gina abubuwan da suka shafe mu da kasarmu, mun dade muna gina rungumar abubuwan da suka fito daga kasashen waje wanda hakan sai ya gina kasashen wasu. Ya kamata a karfafa wa matasa don sus amu kwarin gwiwar tsayawa da kafafunsu. Ya kuma kamata gwamnati ta kawo musu dauki da tallafin jari.

Jama’a na dari-dari game da gudanar da kasuwanci ta Intanet saboda ‘yan damfara, mene ne shawarar ka?

To shi ya sa muka ce wata gada ce da muka tsallaka daga inda muke kasuwanci na da zuwa yadda muke kasuwanci na zamani, wato duk wani dan kasuwa da za mu dora a kan Manhajarmu ta Sayarwa sai mun tabbatar da cewa mun san shi, shi ya sa kuma muke tara ‘yan kasuwa wadanda akwai sanayya tsakaninmu da su wanda ba za ka iya cutar wani mutum ba,ko ko an samu matsalar muna hanyoyin tabbatar da ka shiga hannu.

Mun gode sosai

Nima na gode

Arewa
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    NPA Ta Samo Tallafin Dala Biliyan 1 Domin Aikin Zamanantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Ƙasar Nan

MASU ALAKA

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Tattaunawa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

August 20, 2026
Nijeriya
Tattaunawa

2027: Shugaba Mai Gaskiya Da Hangen Nesa Nijeriya Ke Buƙata —Ahmad Shu’aibu

August 8, 2026
Adadin Masu Amfani Da Intanet A Sin Ya Kai Sama Da Mutane Biliyan 1.12
Tattaunawa

Yadda Na Yi Amfani Da Intanet Wajen Bunƙasa Sana’ata —Fatima Mubaraka

August 8, 2026
Next Post
A Karon Farko, An Kafa Wani Yanki Na “Fitar Da Aikin Ba Da Hidimomin Sin Zuwa Ketare” a CIFTIS Na 2026

A Karon Farko, An Kafa Wani Yanki Na "Fitar Da Aikin Ba Da Hidimomin Sin Zuwa Ketare" a CIFTIS Na 2026

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.