Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC sun yi watsi da shirin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027.
APC ta ce cire tallafin man fetur mataki ne mai tsauri da ya zama dole, wanda ya taimaka wajen karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa ayyukan more rayuwa, ilimi, tsaro da sauran fannoni.
Da yake magana a wani taron APC a Abuja, Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Nentawe Yilwatda, wanda ya wakilci Tinubu, ya ce tattalin arzikin Nijeriya ya samu ci gaba tun bayan fara sauye-sauyen.
Ya ce ajiyar kuɗin ƙasar waje ya kai kusan dala biliyan 52.7, yayin da tattalin arziƙin ƙasar ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100 a zango na biyu na shekarar 2026.
Ya kuma ce hauhawar farashi ya ragu zuwa kusan kashi 15.4 cikin 100.
Yilwatda ya ce Arewa ta amfana sosai daga sauye-sauyen ta hanyar manyan ayyuka kamar bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano, NELFUND da wasu manyan ayyukan tituna da layin dogo.
Ya ce sauye-sauyen za su samar da damar kasuwanci tsakanin Arewacin Nijeriya da maƙwabtan ƙasashe.
Isa Yuguda, Shugaban Kwamitin Amintattu na APC Professionals Forum, ya ce tsohon tsarin tallafin man fetur cike yake da almundahana, ɓarna da rashin kyakkyawan tsarin gudanarwa.
Ya ce gwamnati ta samu rarar sama da Naira tiriliyan 15 tun bayan cire tallafin, yana mai gargaɗin cewa dawo da shi na iya ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati.
Yuguda ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su duba manufofi, ayyukan da aka gudanar da kuma hanyoyin da za su iya magance matsaloli a zahiri yayin zaɓen 2027, maimakon dogaro da alƙawuran samun sauƙi na ɗan wani lokaci.














