Dakarun sojojin sama na kasar Sin, za su halarci bikin nune-nunen jiragen sama na kasa da kasa wanda zai gudana a kasar Masar. Wata sanarwa da rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA ta fitar a yau Lahadi, ta ce za a aike da nau’o’in jiragen sama daban daban, wajen bikin nune-nunen da za a yi tun daga ranar Talata 8 zuwa Alhamis 10 ga watan nan na Satumba.
Sanarwar ta kara da cewa, cikin jiragen da za a tura har da na yaki, da masu gabatar da gargadin gaggawa, da masu karawa jirage mai a sararin sama, da kuma masu saukar ungulu.
Wannan ne karo na biyu da za a gudanar da wannan bikin nune-nunen jiragen sama, a filin jirgin saman kasa da kasa na El Alamein, bayan gudanar irinsa na farko a shekarar 2024. A yayin bikin nune-nunen na farko ma jiragen sojin saman kasar Sin sun shiga an dama da su, inda jiragen yaki samfurin J-10, da wani jirgin samfurin Y-20, babban jirgin dakon kayayyaki mafi girma kirar kasar Sin suka gudanar da atisaye.
A bana ake cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Masar, kuma sassan biyu sun gudanar da jerin ayyukan musaya tsakanin kasashen biyu. A watan da ya gabata, rundunonin sojin saman kasashen biyu, sun kaddamar da jerin atisaye bisa taken “Eagles of Civilization-2026” a kasar Masar. (Saminu Alhassan)














