Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta yi gargadi ga jama’a kan shafukan sada zumunta na bogi da ke amfani da sunanta, tambarinta da hotonta na hukuma wajen yada bayanai marasa izini da kuma wadanda za su iya yaudarar al’umma.
Hukumar, a cikin sanarwar gargadi da shugaban sashen yada labarai da wallafe-wallafenta, Shafii Sani Mohammed, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ta nuna damuwa kan ayyukan wasu mutane da kungiyoyi da ke gudanar da shafukan Facebook, kungiyoyi da sauran kafafen sada zumunta ba tare da izini ba, suna amfani da sunan hukumar.
NAHCON ta bayyana cewa wadannan shafuka ba mallakarta ba ne, ba ita ke gudanar da su ba, ba ta amince da su ba, kuma ba ta ba su izinin amfani da sunanta ba.
Ta yi gargadin cewa irin wadannan shafuka na iya haifar da tunanin cewa suna da alaka da hukumar, lamarin da zai iya jefa jama’a cikin rudani tare da yaudarar masu neman sahihan bayanai.
Domin kauce wa wannan rudani, hukumar ta bayyana cewa hanyoyin sadarwa da ta amince da su sun hada da shafinta na yanar gizo, www.nahcon.gov.ng, da shafukanta na Facebook, X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) da Instagram, wadanda duk suke amfani da sunan @nigeriahajjcom, da kuma tasharta ta YouTube, youtube.com/@nahcon.
Hukumar ta bukaci jama’a da su rika samun bayanai game da ayyukanta, musamman harkokin Hajji da Umrah, daga wadannan sahihan kafafen sadarwa da ta tabbatar da ingancinsu kawai.
Haka kuma, ta shawarci ‘yan Najeriya da su yi watsi da sanarwa, wallafe-wallafe da ikirarin da ake yadawa ta shafuka da kungiyoyin da ba ta amince da su ba.
Ta kuma gargadi jama’a da su guji yadawa ko kara yada bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, wadanda za su iya yaudarar al’umma ko kuma bata sunan hukumar.
NAHCON ta kara kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani shafin sada zumunta ko kungiya da ke amfani da sunanta, tambarinta ko hotonta ba tare da izini ba.
Haka kuma, ta gargadi masu gudanar da irin wadannan shafuka da kungiyoyi da su gaggauta dakatar da amfani da sunan hukumar ta hanyar da ba ta dace ba, tare da hana amfani da tambarinta ba tare da izini ba ko yada bayanan da za su iya cutar da jama’a a karkashin sunanta.
Hukumar ta bayyana cewa tana da hakkin daukar matakan gudanarwa da na shari’a da suka dace domin kare sunanta, martabarta da sauran muradunta na hukumance.
A karshe, NAHCON ta sake jaddada muhimmancin dogaro da sahihan hanyoyin sadarwarta wajen samun ingantattun bayanai, sahihai kuma tabbatattun bayanai game da ayyukan Hajji da Umrah.













