A yau Asabar, kasar Sin ta dauki wani muhimmin mataki na tabbatar da zamanantarwa mara gurbata muhalli, yayin da dokarta mai alfanu kan kiyaye muhalli da tsarin rayuwar halittu ta fara aiki a hukumance; matakin da ya kara karfafa ginshikin doka na tabbatar da zaman jituwa a tsakanin dan ’Adam da yanayi na sali.
Wadda babbar majalisar dokokin kasar Sin ta amince da ita a watan Maris ta bana; dokar ita ce ta biyu da kasar Sin ta kafa a hukumance bayan kundin dokar da ta shafi tsarin rayuwar fararen hula.
Dokar ta kunshi sassa 1,242 da aka karkasa zuwa babi biyar, wadanda suka shafi batutuwa kamar dakile gurbata yanayi, da kare tsarin rayuwar halittu, da kuma samun ci gaba mara gurbata muhalli da rage fitar da hayakin carbon mai bata yanayi, da sauransu.
Har ila yau, duk dai a yau Asabar kasar Sin tana gudanar da bikinta na ranar muhalli ta kasa karo na hudu, karkashin taken “Gina harsashin ci gaba mara gurbata muhalli domin zamanantarwar kasar Sin.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)














