Doma United ta cigaba da jagorantar teburin Firimiyar Nijeriya (Euro Match Premier League) bayan ta doke Enyimba United da ci 2-0 a filin wasa na Pantami da ke Gombe a ranar Asabar.
wannan ne karo na biyu da Enyimba United wadda ta lashe gasar sau 9 tayi rashin nasara a kakar wasan ta bana, wanda hakan ya janyo ta koma matsayi na 20 a teburin gasar ta Euro Match Premier League.
Doma United wadda ta samu nasarar buga babbar gasar ta kasa a wannan kakar ta bana ta cigaba da zama a matsayi na daya a teburin gasar bayan samun nasara sau uku a jere, inda ta hada maki 9 da kwallaye 5 rigis a wasanni uku da ta buga.
Doma ta doke Sporting Lagos a wasan farko da suka buga daci 2-0 a Gida, kafin ta doke Inter Lagos daci 1-0 a wasa na biyu da ta buga.
Nasarar da ta samu a kan Enyimba ta tabbatar da matsayinta a saman teburin gasar, a daya bangaren kuma, Enyimba ta sake fuskantar koma baya, inda ta fara kakar wasa ta bana da rashin nasara a hannun Niger Tornadoes daci 2-0.
Hukumar dake shirya gasar ta dage wasan Enyimba da Shooting Stars sakamakon wasannin kasa da kasa da Enyimbar ke bugawa.













