Wani tsohon Kwamishinan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe, Hon. Muhammad Ismail City, wanda aka fi sani da Katukan Akko, ya fice daga Jam’iyyar APC, tare da bayyana goyon bayansa ga takarar Farfesa Isa Ali Pantami a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP.
Katukan Akko, wanda ya taɓa zama shugaban ƙaramar hukumar Akko kuma ɗan kasuwa, ya bayyana goyon bayansa ga Pantami a hukumance yayin wata ganawa da tsohon ministan a ofishinsa, ranar Asabar.
Tsohon kwamishinan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan nazarin yanayin siyasar Jihar Gombe da kuma gamsuwarsa cewa jihar na buƙatar shugaba mai gaskiya, ƙwarewar gudanar da mulki da kuma hangen nesa wajen ciyar da jihar gaba.
Ya bayyana cewa, ƙwarewar da ya samu a harkokin mulkin ƙananan hukumomi da gudanar da zaɓe ta ba shi damar fahimtar irin halayen da shugaba ke buƙata domin inganta tattalin arziƙi, tsaro da hukumomin gwamnati.
Katukan Akko ya ƙara da cewa Gombe na cikin wani yanayi na siyasa da ke buƙatar shugaba mai nagarta, ƙwarewar hulɗa da ƙasashen duniya da kuma tarihin aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo ci gaba.
ADVERTISEMENT













