ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

by Muhammad
2 months ago

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, ya bayyana cewa irin jajircewar da al’ummar ƙasarsa suka nuna wajen dakile yunƙurin juyin mulki na ranar 15 ga Yulin 2016 ita ce mafi girman misalin kare dimokuraɗiyya a tarihin duniya.

A cikin saƙon da ya fitar domin tunawa da cika shekaru goma da yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, Erdoğan ya ce ranar 15 ga Yuli ta kasance ɗaya daga cikin ranakun da suka fi muni a tarihin siyasar Turkiyya, amma kuma ta zama wata rana da ta nuna ƙarfi da jajircewar al’umma wajen kare dimokuraɗiyya.

Ya zargi ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Fetullahist Terrorist Organisation (FETO) da shirya yunƙurin juyin mulkin, yana mai cewa manufarsu ita ce jefa ƙasar cikin rikici na dogon lokaci tare da tauye ikon mallakar ƙasar.

ADVERTISEMENT

Erdoğan ya ce: “Ta hanyar tsayawa tsayin daka domin kare ‘yancinsu da makomarsu tare da fuskantar masu juyin mulki, al’ummar Turkiyya sun nuna wa duniya cewa muradin jama’a ba zai taɓa rushewa a wannan ƙasa ba,”

“Hikima, jarumtaka da hangen nesan da al’ummar Turkiyya suka nuna a daren 15 ga Yuli ba su da tamka a tarihin dimokuraɗiyyar duniya.” A cewar Erdoğan.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Shugaban ya bayyana cewa yunƙurin juyin mulkin bai kasance kawai wani yunƙuri na sojoji na ƙwace mulki ba, illa ya kasance wani hari da aka kai kan ‘yancin kai da cikakken ikon Turkiyya. Ya ce Fadar Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokokin Turkiyya na daga cikin manyan wuraren da aka yi niyyar kai wa hari, saboda suna wakiltar ikon jama’a da dimokuraɗiyya.

Erdoğan ya tuna da jawabin da ya yi wa al’umma a daren juyin mulkin, inda ya jaddada cewa babu wata hukuma da ya fi girmamawa kamar ikon jama’a.

Ya ce ya yi wannan furuci ne cikin cikakken tabbacin cewa al’ummar Turkiyya za su tsaya tsayin daka wajen kare muradinsu da tsarin dimokuraɗiyya.

A ƙarshe, shugaban ya yaba wa ‘yan ƙasar da suka fito kan tituna cikin ƙarfin hali da azama domin fuskantar masu juyin mulki, duk da haɗarin rasa rayukansu, yana mai cewa wannan ya tabbatar da ƙudurin al’ummar Turkiyya na kare dimokuraɗiyya da ’yancin ƙasarsu.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.