ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dunkulewar Kasa Shi Ne Burin Bai Daya Na Jama’ar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan

by Sulaiman
3 months ago
Taiwan

An bude taro na 18 na tattaunawa da inganta musaya tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, wanda ke kara nuna kudurin babban yankin Sin na hada kan al’ummominta don cimma dunkulewar dukkan yankunanta wuri guda da cimma babban burin raya kasa.

Kasancewar Taiwan wani bangare na Sin ba wani sabon abu ba ne, amma wasu ’yan tsiraru na biye wa rudin masu zugasu, inda suke ganin kamar za su iya ballewa daga babban yankin.

Taron a lardin Fujian, wanda aka fara yinsa tun a shekarar 2009, a bana ya samu halartar adadi mai yawa na wakilai daga dukkan fannoni na yankin Taiwan. Kuma tun bayan kafuwar Fujian matsayin yankin gwaji na inganta raya gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan a 2023, an samu nasarori da dama. Misali masu ziyara daga yankin Taiwan a lardin na Fujian ya kai sama da miliyan 1.04 a bara, wanda ya kusa ninka adadin na 2023.

ADVERTISEMENT

Haka kuma cikin shekaru 3 da suka gabata, sama da sabbin kamfanoni 7,100 masu jarin Taiwan aka kafa a lardin. Shin duk me hakan ke nufi? Wannan ya nuna wa mahukuntan yankin Taiwan da masu ingiza su da ma duniya baki daya cewa, muradun al’ummar Sinawa iri daya ne, kuma burinsu ma haka, watau dunkulewar baki dayan kasar wuri guda da karfafa zumunci da dangantaka a matsayinsu na Sinawa.

Haka kuma, ya nuna cewa jama’ar Taiwan sun aminta da babban yankin wajen kare su da samar musu damarmakin ci gaba. Baya ga kasancewarsa sako mai karfi ga masu tsoma baki cewa, su ne za su ji kunya a duk lokacin da burin dinkewar dukkan yankunan kasar Sin ya tabbata.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Tabbas yadda taron ke samun nasarori ta fuskar inganta mu’amala da musaya, tsakanin jama’ar bangarorin biyu, abun burgewa ne, wanda ke kara nuna kauna da kishinsu ga kasarsu. Tabbas wadannan nasarori na da nasaba da irin hangen nesan babban yankin kasar na karbar bancin wannan taro a duk shekara, wadda alama ce da ke nuna matsayinta na mai sanin ya kamata, wadda ba ta watsi da al’ummarta.

Haka kuma, yunkuri ne da zai kara fahimtar da jama’ar Taiwan kyakyyawar manufar babban yankin game da su. Ko da yake duba da adadin masu ziyara da zuba jari da kafa kamfanoni har ma da mahalarta taron, za mu iya cewa, sun fahimci hakan, sun san kyakkyawar niyyar Sin ta bunkasa ci gaban yankunanta.

Ya kamata mahukuntan Taiwan su gane cewa, yunkurinsu ba zai haifar da komai ba sai karin rashin farin jini da cikas a gare su. Kuma babban yankin kasar Sin shi ne babban mai son ganin ci gaban Taiwan da zaman lafiya da kwanciyar hankalinsa. (Fa’iza Mustapha)

Taiwan
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026

Next Post
2023: Tinubu Ya Zaɓi Kashim Shettima A Matsayin Mataimaki

Shin Har Yanzu Shettima Ne Abokin Takarar Tinubu?

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.